Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane 20, ta raba dubu 3 da muhallansu a Yobe
An tabbatar da mutuwar aƙalla mutane 20 sakamakon rugujewar gidaje sanadiyar mamakon ruwan sama, makonni 2 da suka gabata a garin Gashuwa, shelkwatar ƙaramar hukumar Bade ta jihar Yobe.
Shugaban ƙaramar hukumar, Babagana Ibrahim ya shaidawa wakilin tashar talabijin ta Channels cewa, galibin mazauna garin na samun mafaka ne a wasu sansanoni 3 da aka ware.
A cewarsa, gwamnati na samar da muhimman buƙatun ‘yan gudun hijirar da suka haɗa da kayan abinci da magunguna da kayan tsaftace muhalli da ruwan sha da abinci mai tsafta domin magance barkewar cututtuka.
KU KUMA KARANTA:Ambaliyar ruwa a Arewa ta kashe mutum 49, ta raba 41,344 da muhalli – NEMA
Babagana Ibrahim ya kuma nemi karin tallafi daga gwamnatin tarayya da hukumomin bada agaji.
An ruwaito shi yana cewa, “adadin wadanda suka rasa muhallansu ya karu zuwa kusan dubu 3, muna bukatar gwamnatin tarayya da hukumomin bada agaji su tallafawa jihohi da kananan hukumomin da ibtila’in ambaliyar ruwa ta afkawa ta hanyar sama musu da kayan agaji.”
Ana samun ruwan sama a ‘yan kwanakin nan kuma gidaje da dama musamman na kasa ke rushewa. Da safiyar yau kawai, an tabbatar da mutuwar mutane 4 a Gashua.”