‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar mawaƙi Rarara

0
97
'Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar mawaki Rarara

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar mawaƙi Rarara

Daga Idris Umar, Zariya

Labarin dake zuwa mana yanzu shine ’yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar shahararren mawaƙin siyasa, Dauda Kahutu Rarara.

Kamar yadda akace an yi garkuwa da Hajiya Hakima Adamu ne a gidanta da yankin Kahutu a ƙaramar hukumar Ɗanja ta jihar Katsina, kamar yadda aka tseguntawa manema labarai

Wasu mutane a ƙauyen sun ce da misalin karfe daya na dare ne dandazon ’yan bindiga suka kutsa gidan dattijuwar suka yi gaba da ita.

“A kafa suka zo, kuma kasancewar ba su yi harbi ba a lokacin da suka kai harin suka yi garkuwa da ita cikin ’yan mitoci. Dattijuwar ba ta yi musu turjiya ba a lokacin da suka ce ta biyo su.

KU KUMA KARANTA: Ƴan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai da dama a jihar Delta

“Duk da cewa ’yan bindigar sun samu wasu mutane a gidan, amma mahaifiyar Rarara kaɗai suka ɗauka suka tafi da ita.

“Babu wani yunƙuri da aka yi na tunkarar ’yan bindigar a lokacin da suke tafiya da ita saboda suna dauke da bindigogi,” in ji wani mazaunin kauyen na Kahutu, kamar yadda majiyarmu ta jiyo.

Leave a Reply