Gwamnatin tarayya ta hana amfani da sirinjin allura na ƙasashen waje a manyan asibitoci ƙasar

0
474

Gwamnatin tarayya ta umurci dukkan shugabannin manyan asibitocin gwamnatin tarayya da su sayi allura da su riƙa amfani da allura da da ake ƙera su a gida kuma hukumar NAFDAC ta amince da su.

Sabuwar umarnin na ƙunshe ne a cikin wata takardar ga dukkan shugabannin asibitoci mai ɗauke da sa hannun ƙaramin ministan lafiya, Dakta Tunji Alausa, a yau Juma’a.

Ministan ya ce an ba da wannan umarnin ne domin bunƙasa samar da kayayyakin da ake ƙera wa a cikin gida da kuma kare masana’antun ƙasar daga kwararar kayayyakin ƙasashen waje.

Sanarwar ta kuma umarci hukumar ta NAFDAC ta dakatar da bayar da lasisin shigo da allura da sirinji da aka ƙera daga ƙasashen waje.

Alausa ya ce ɓangaren lafiya ya gano masana’antar har haɗa magunguna ta cikin gida da ke samar da allura da sirinji waɗanda ke cikin matsala matuƙa saboda wannan mummunar harkar.

Ya kuma ce daga cikin kamfanonin har haɗa magunguna guda tara na cikin gida da suke samar da allura da sirinji shekaru takwas da suka gabata, shida sun rufe saboda zubar da kayayyakin da ba su da inganci a kasuwa.

KU KUMA KARANTA:NAFDAC ta haramta amfani da maganin tari na yara na kamfanin J&J

“Shugaban ƙasa ya ba da umarnin cewa dole ne a daina wannan. Dukkanmu mun amince da ɗaukar matakan da suka dace don magance wannan mummunan yanayi cikin gaggawa.

“A bisa haka, hukumar ta NAFDAC ta dakatar da bayar da lasisin shigo da allura da sirinji da aka ƙera daga ƙasashen waje.

“Haka kuma shi ne a soke jerin sunayen kamfanonin da ke da hannu wajen shigo da waɗannan kayayyakin da ke ci gaba,” in ji shi

Leave a Reply