’Yan fashi sun kai hari bankuna da ofishin ’yan sanda a Kogi

0
138

Wasu ’yan fashi da makami sun kai farmaki bankuna da ofishin ’yan sanda a garin Anyigba da ke Karamar Hukumar Dekina a Jihar Kogi.

Bayanai sun ce ’yan fashin sun kai farmakin ne da misalin ƙarfe 5:00 na Yammacin wannan Alhamis ɗin inda suka riƙa harbe-harbe kan mai uwa da wabi.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, ’yan fashin sun soma kai farmakin ne kan ofishin ’yan sanda, sannan daga bisani suka waiwaya kan bankunan waɗanda suka riƙa tayar da nakiyoyi.

Wani ganau ya ce a halin yanzu ana cikin ruɗani yayin da mazauna ke tserewa domin neman mafaka a ƙauyukan da ke makwabtaka da su.

KU KUMA KARANTA: An cafke ‘yan fashin babur da ke busa barkono a fuskar ‘yan okada kafin su karɓe babur

“A yanzu da nake magana da kai, ana ci gaba da harbe-harbe kuma ba mu san yanayin da ake ci gaba.

“Mun samu labarin an kai harin bam a ofishin ’yan sanda na hanyar Idah da ke Anyigba, sannan ‘yan fashin sun nufi bankin Access, bayan sun yi wa wasu bankunan fashi da makami,” a cewar Mohammed Alabi, mazaunin Anyigba.

Ya ƙara da cewa “har yanzu babu wani tabbataccen labari kan lamarin saboda babu wanda zai iya fita a yayin da har yanzu ana jin ƙarar harbin bindiga daga gefen garin.

“Ba zan iya cewa komai kan waɗanda lamarin ya rutsa da su ta fuskar ƙarar kwana ko samun rauni. Amma dai har yanzu ’yan fashin na nan saboda daga inda muka laɓe ma muna jiyo ƙarar harbe-harbe,” a cewarsa.

An tuntubi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP William Aya, amma bai ɗauki waya ko amsa sakon kar ta kwana ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Leave a Reply