Daga Ibraheem El-Tafseer
Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa reshen jihar Jigawa ta yi watsi da tukwicin 10,000 da gwamnatin jihar za ta bai wa ma’aikatanta a matsayin kuɗin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.
Wannan yana ƙunshe a cikin wata sanarwar da aka saki bayan kammala taron ƙungiyar da aka yi ranar Talata a Dutse.
Sanarwar wadda shugabannin ƙananan hukumomi da kuma sakatarorin ƙungiyar ‘yan ƙwadago ta NLC da TUC reshen jihar suka saka hannu ta fasalta yadda gwamnatin ta yi azarɓaɓin yanke hukunci kan ba da tukwicin tun da ba su cimma yarjejeniya ba.
A farkon makon nan ne dai gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ya amince da biyan ma’aikatan jihar kudi 10,000 a duk wata a tsawon watanni uku, kafin gwamnatin tarayya ta fito da tsarin sabon albashi.
KU KUMA KARANTA: Malaman firamare a Abuja sun gudanar da zanga-zanga, kan rashin biyan haƙƙinsu na albashi
A makon da ya gabata ne dai gwamnatin tarayyar ƙarƙashin mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima ya ƙaddamar da kwamitin domin yin duba ga albashin da ake biya mafi ƙanƙanta a Najeriya.









