INEC ta cire PDP a jerin jami’iyyun da za su shiga zaɓe a Filato

0
94

Daga Maryam Umar Abdullahi

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC, ta cire jami’iyyar PDP a jerin jami’iyyun da za su shiga zaɓen da za ta gudanar na ‘yan majalisun tarayya a shiyyar Arewacin jahar Filato.

Gudanar da zaɓen ya biyo bayan shara’ar da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke, inda ta cire sanata mai wakiltar Filato ta Arewa, Simon Mwadkon da ɗan majalisa mai wakiltar Bassa da Jos ta Arewa, a Majalisar wakilai, Musa Agah, bisa hujjan cewa jami’iyyar PDP ba ta da shugabanni kafin gudanar da zaɓen na 2023.

Mataimakin kakakin jami’iyyar PDP a jahar Filato, Alhaji Abdullahi Garba Mai Rake yace tun suna jin ƙishin-ƙishin har dai ya tabbata ba sunan jami’iyyar su a cikin zaɓen na ranar Asabar.

KU KUMA KARANTA: Gamayyar ƙungiyoyin farar hula ta Najeriya ta ɗorawa hukumomi alhakin rashin tsaro

Shugaban ƙungiyar gamayyan jami’iyyu ta IPAC a jahar Filato, Abubakar Dogara yace ba su da hurumin canza matakin da hukumar zaɓen ta ɗauka, sai dai jama’a su yi haƙuri su gudanar da zaɓen cikin lumana.

Mai fashin baƙi kan lamura kuma shugaban ƙungiya mai zaman kanta ta CLEEN, Gad Shamaki Peter ya ce kotu ce kaɗai za ta ƙwato wa PDP ‘yancin ta.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa ta ce zaɓen na ranar Asabar zai cike guraben sanatoci uku, da wakilan Majalisar tarayya goma sha bakwai, da ‘yan majalisun dokoki jaha guda ashirin da takwas a ƙananan hukumomi tamanin a jihohi ashirin da shida na Najeriya.

Leave a Reply