Yobe tana zaburar da masu zuba jari a cikin irin riɗi, ƙaro da kuma sarrafa su

0
161

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni CON, ya ce gwamnati za ta samar da yanayin da zai sa masu zuba jari su zuba jari kai tsaye wajen samar da iri da sarrafa irin Riɗi da Ƙaro da kuma kiwo domin bunƙasa tattalin arziƙin jihar.

Gwamna Buni, yayin da yake bayani game da matsayin jihar Yobe a matsayin jiha ta 9 mai sauƙin gudanar da kasuwanci a Najeriya, ya ce “domin mu cimma wannan nasara bayan da aka ɗauki tsawon lokaci ana fama da matsalar tsaro, shi ne ya sa gwamnatinmu ta ƙara ƙaimi.

Riɗi

“Wannan ya nuna cewa jihar Yobe tana samun ci gaba cikin sauri, kuma ta zama jiha mai son kasuwanci,” in ji Buni.

Ya bayyana cewa, tare da ingantuwar harkokin tsaro da ɓullo da wasu guraben ayyukan yi da gwamnatin jihar ke yi, jihar Yobe ta himmatu wajen ganin ta zama jaha kan gaba a harkokin cinikayya da kasuwanci.

Ƙaro

“Mun kammala tare da ƙaddamar da filin jirgin saman dakon kaya na ƙasa da ƙasa domin sauƙaƙa harkokin kasuwanci da zirga-zirga a ciki da wajen ƙasar nan.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin jihar Yobe ta rarraba kayan aikin gona don inganta noma a jihar

“Gwamnatinmu ta gina kasuwannin zamani da kayayyakin da wuta ba za ta iya ƙona wa ba, ko da gobara ta auku, don sauƙaƙa wa da tallafa wa ‘yan kasuwa,” inji shi.

Ya bayyana cewa gwamnatinsa na tuntuɓar ƙasashen duniya domin ganowa tare da yin amfani da damar da ake da su wajen noma da sarrafa nau’in Riɗi, ƙaro da kuma kiwo.

“Gwamnati za ta inganta dukkan ɓangarorin haɗin gwiwa don gudanar da ayyuka masu ƙarko da inganci don bunƙasa harkokin kasuwanci a jihar.

“Ina so in tabbatar muku da cewa, gwamnati za ta ci gaba da samar da ababen more rayuwa don mayar da jihar Yobe cibiyar kasuwanci da ke haɗa Arewa da sauran ƙasashe, wajen noma da sarrafa irin Riɗi, Ƙaro, da kuma Kiwo,” inji Gwamna Buni.

Leave a Reply