NAFDAC da Ma’aikatar lafiya a jihar Yobe sun yi taro kan cutar tamowa

2
304

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasa (NAFDAC) tare da haɗin gwiwar ma’aikatar lafiya ta jihar Yobe sun haɗa ma’aikatan lafiya kan hanyoyin magance matsalar rashin abinci mai gina jiki ga yara a faɗin jihar.

Misis Rahila Maishanu, jami’ar kula da hukumar ta NAFDAC, ce ta bayyana hakan a ranar Talata a wajen bikin ƙaddamar da horarwa na tsawon kwanaki uku na ƙarfafawa da sa ido ga kwamitin fasaha na jihar Yobe, a Damaturu.

Ta ce matakin zai inganta sakamakon shayarwa bisa bin ƙa’idar kasuwanci ta ƙasa da ƙasa na maye gurbin nono (BMS).

2 COMMENTS

Leave a Reply