Masallacin ƙasa na Abuja ya bayar da tallafin abinci ga ‘yan gudun hijira 400

1
638

Mu’assasar Da’awah, walwala da jin daɗi (ANMDWF) na masallacin ƙasa dake Abuja ta raba tallafin kayan abinci ga ‘yan gudun Hijira su 400 a yayin rabon kayan abinci ga mabuƙata a Abuja ranar Asabar.

Abbas Jimoh na Gidauniyar Da’awah ta ƙasa da ke Abuja, (ANMDWF), ta bayar da tallafin kayan abinci ga musulmi sama da 400 a babban birnin tarayya Abuja.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Yobe ta ware miliyan 73 don ciyar da masu azumi a watan Ramadan

Shugaban Gidauniyyar, Dakta Muhammad Kabir Adam ne ya jagoranci sauran jami’an gidauniyar wajen rabon kayayyakin da aka gudanar a sansanin ‘yan gudun hijira na Area 1, da ‘yan gudun hijira da kuma a ɗakin taro na babban masallacin Abuja na ƙasa a Abujan.

A cewar sa, an yi hakan ne don ciyar da al’ummar musulmin da ke da buƙatar abinci domin samun sauƙin azumin watan Ramadan.

Shi ma da yake jawabi yayin atisayen, Sakataren ƙungiyar ta (ANMDWF), Jafaru Umoru, ya ce matakin na daya daga cikin ayyukan gidauniyar.

“A shekarar da ta gabata ne Murshid na masallacin Abuja na ƙasa Farfesa Shehu Said Galadanchi ya kafa gidauniyar domin gudanar da ayyukan da’awa da walwala.

A cikin wannan Ramadan, muna haɗa kai da ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyi,” inji shi. Ya ce: “Abin da muke bayarwa a yau shi ne shinkafa, semovita, mai da sauran kayan abinci na abinci.

Tun da farko mun je sansanin ‘yan gudun hijira da ke Area 1 inda muka raba wa ‘yan gudun hijira sama da 100.” Ya kuma ce bayan samar da kayan abinci, za a horar da wasu adadin mutane da kuma ba su damar tsayawa da kansu da kuma samun damar ɗaukar wasu ma’aikata.

Ya kuma buƙaci masu hannu da shuni da ƙungiyoyi da su taimaka wa mabuƙata ko dai a cikin watan Ramadan da kowane lokaci domin bautar Allah.

1 COMMENT

Leave a Reply