Ramadan: Gwamnatin Kano ta amince da hutun mako 3 ga makarantu

2
418

A jiya Alhamis ne gwamnatin jihar Kano ta amince da ranar 7 ga watan Afrilu domin fara hutun wa’adi na biyu na watan Azumin Ramadana a makarantun gwamnati da masu zaman kansu a faɗin jihar Kano.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar ilimi Aliyu Yusuf ya fitar ranar Alhamis a Kano.

Gwamnati ta umarci iyaye da masu kula da ɗaliban da ke makarantun kwana da su kai ɗaliban ɗakunansu a safiyar Juma’a.

KU KUMA KARANTA: A hankali ya kamata ku aiwatar da manufar kashless – Sarkin Kano ga CBN

A cewarsa, duk ɗaliban da ke makarantun kwana za su koma makarantunsu a ranar 30 ga watan Afrilu, yayin da ɗaliban za su koma ranar 2 ga watan Mayu, yana mai gargaɗin cewa za a ɗauki matakin ladabtarwa a kan waɗanda suka gaza yin hakan.

“Ɗalibai, iyaye da masu kula dasu, su tabbatar da bin ƙa’idojin da aka amince da su na komawa aiki,” in ji ta, tare da yi wa ɗaliban fatan samun nasara a hutun.

2 COMMENTS

Leave a Reply