A hankali ya kamata ku aiwatar da manufar kashless – Sarkin Kano ga CBN

2
218

Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi kira ga babban bankin Najeriya (CBN) da kuma bankunan kasuwanci da su riƙa bin manufofin janye takardun kuɗi zuwa amfani da kuɗin hanyar fasahar zamani wato kashless sannu a hankali domin al’ummar ƙasar nan su rugumi tsarin tare da sanin sabbin sauye-sauyen da ke tattare da manufofin.

Sarkin ya yi wannan kiran ne a lokacin da tawagar kwamitin bankunan Najeriya ƙarƙashin jagorancin babban bankin Najeriya CBN suka kai ziyarar ban girma a fadarsa da ke birnin Kano, a ranar talata.

Ya ce duk da cewa manufar tana da kyau kuma za ta kawo ci gaba mai kyau a ƙasar, amma ta jefa mutane cikin wahala domin an ɓullo da ita cikin gaggawa, inda ya buƙaci a yi hakuri da jama’a har su karɓi shirin, musamman a yankunan karkara.

KU KUMA KARANTA: Mun bada isasshen lokaci don haka babu ja da baya kan daina karɓar tsoffin kuɗi- CBN

A cewar sarkin, maimakon gaggauta aiwatar da manufofin, ya kamata bankuna su fara wayar da kan jama’a da wayar da kan jama’a game da sauye-sauye masu kyau da jama’a za su iya samu idan sun rungumi tsarin, ya kuma ƙara da cewa kamata ya yi su saurari ra’ayoyin jama’a domin hakan zai taimaka musu, don samun nasara a cikin manufofin shirin.

Tun da farko a nasa jawabin, mataimakin daraktan babban bankin na CBN, wanda kuma shi ne jagoran tawagar, Muhammed Hamisu Musa ya ce, manufar ziyarar ita ce neman alfarmar sarkin, sannan kuma ya buƙace shi da ya faɗakar da jama’a su rungumi tsarin kuɗin na kashless domin shirin ya sami gindin zama.

2 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here