Yadda ’yan sanda suka kama Murja ‘yar tiktok a Otal

0
332

Jami’an ‘yan sanda sun kama fitacciyar jaruma a dandalin tiktok mai suna Murja Kunya a otal ɗin Tahir da ke Kano.

‘Yan sandan sun kama ta ne a lokacin da take ƙoƙarin kamawa baƙinta da suka zo daga nesa da kusa ɗakuna domin bikin zagayowar ranar haihuwarta da aketa yaɗawa.

Idan mai karatu zai tuna, Neptune Hausa ta rawaito a watan Satumban shekarar da ta gabata cewa wata kotun shari’a ta rubutawa kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano da ya kama Murja Kunya tare da wasu ‘yan TikTok da ake zargi da lalata tarbiyar al’umma.

KU KUMA KARANTA:Muna neman Safara da Mr 442 ruwa a jallo- Afakallahu

Sauran ‘yan TikTok ɗin da ke cikin wasikar sun haɗa da Mr 442, Safara’u, Ɗan Maraya, Amude Booth, Kawu Ɗan Sarki, Ado Gwanja, Ummi Shakira, Samha Inuwa da Babiana.

“Sakamakon ƙarar da Muhd ​​Ali Hamza Esq, Abba Mahmud, Esq, Sunusi I. Umar Esq, Abba, A.T Bebeji Esq, B. I Usman Esq, Muhd ​​Nasir Esq, L.T Dayi Esq, G.A Badawi da Badamasi Suleiman Gandu Esq suka gabatar, Alƙalin kotun mai shari’a ya bada umarni a Bichi reshen Kano don rubutawa tare da roƙon ku da ku binciki waɗanda ake zargin don ɗaukar matakin da ya dace,” daga wani ɓangare na wasiƙar.

Har ila yau, Neptune Hausa ta kuma kawo rahoton cewa an kama Mista 442 a watan Nuwamban 2022 a Jamhuriyar Nijar a lokacin da yake ƙoƙarin samun Visa zuwa Dubai ta hanyar amfani da takardun bogi na ƙasar.

KU KUMA KARANTA:Yadda aka kama Mr 442 da abokinsa da takardun bogi a Nijar

A watan Nuwamban shekarar da ta gabata ne wata kotun majistare ta jihar Kano ta yanke wa wasu matasa biyu Mubarak Isa da Nazifi Bala hukuncin bulala 20 na ranka da kuma yi wa al’umma hidima na tsawon kwanaki 30 bisa samun su da laifin yin wasan barkwanci na TikTok kan gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje.

An yanke wa waɗanda ake tuhumar hukuncin ne bisa tuhume-tuhume biyu da suka shafi ɓata suna da kuma tada hankalin jama’a.

Babban Alkalin Kotun, Aminu Gabari, ya yanke wa mutanen biyu hukuncin bulala 20 na sanda da kuma yi wa al’umma hidima na tsawon kwanaki 30, ciki har da shara da wanke-wanke na harabar kotun da ke Noman’s Land.

Mai shari’a Gabari ya kuma umarci waɗanda aka yanke wa hukuncin da su biya tarar Naira 20,000 ko wannensu, da yin bidiyo a shafukan sada zumunta su nemi gafarar Gwamna Ganduje.

KU KUMA KARANTA: <strong>Kotu ta yanke wa su Mubarak Pikin hukuncin bulala ashirin</strong>

‘Yan sandan a Kano sun Kama Murya Kunya ne a lokacin da take tsaka da shirye shiryen bikin zagayowar ranar haihuwarta, suka ce an sami wani manyyan mutane a Kano da suke ta ƙoƙarin ganin an sake ta

Leave a Reply