Yadda uba ya haɗa baki da ɗansa ya yi wa ‘yarsa ciki

0
527

Jami’an ‘yan sanda a jihar Legas, sun kama wani mutum mai shekaru 62, mai suna, Kehinde Adeleke da ɗansa, mai suna Ayomide Adeleke, mai shekaru 19 bisa zargin laifin haɗa baki tare da yin lalata da ‘yar cikinsa har ta ɗauki juna biyu.

Lamarin da ya faru a gidan da suke zaune, a unguwar Ijeshatedo a Legas.

Ɗiyar mutumin ta kasance cikin mawuyacin hali a sakamakon yawan lalatar da mahaifinta da ɗan uwanta ke yi da ita, kuma sakamakon gwajin da likitoci suka yi mata ya nuna cewa tana dauke da juna biyu, kuma ba a iya tantance ko wanene ke da alhakin cikin a tsakanin mahaifinta da ɗan uwanta, kasancewar su duka biyun ke yin lalata da ita.

Rundunar ‘yan sandan ta yi zargin cewa, mutumin mai suna Adeleke da ɗansa Ayomide, sun haɗa baki, suka rufe abun, har sai da ta samu juna biyu, sannan ta bayyana abinda ya faru.

An kai karar waɗan da ake zargin ne ga ‘yan sandan yankin, inda aka kama su tare da miƙa su sashin kula da jinsi na rundunar ‘yan sandan domin ci gaba da gudanar da bincike.

Bayan kammala bincike ne ‘yan sandan suka same su da laifi, inda daga bisani suka gurfanar da su a gaban kotun, majistare da ke Ogba bisa laifin da ake zarginsu da aikatawa, wanda hukuncin zai iya kaiwa ɗaurin shekaru da yawa a gidan yari ko kuma ɗaurin rai da rai idan har kotu ta same su da laifin.

Sai dai a lokacin da aka gurfanar da su gaban kotu, kotun ba ta amsa kararsu ba bayan da mai gabatar da kara, Insifekta Lucky Ihiehie, ya buƙaci kotun ta mika lamarin ga sashin binciken shari’a na DPP domin neman shawara, tun da laifin da ake zarginsu da aikatatwa babban laifi ne.

Mai shari’a, Mrs O.A. Layinka, ta bayar da umarnin a tsare su a gidan yari da ke Kirikiri a Legas, ba tare da zabin beli ba, har sai sakamakon shawarar da DPP ta bayar, yayin da ta umurci mai gabatar da ƙara da ya kwafi fayil din tare da aika wa DPP don neman shawara.

An ɗaga cigaba da sauraron ƙarar har zuwa ranar 20 ga Disamba, 2022, don jiran rahoton shawarar DPP , wanda zai tabbatar da ko za a mika batun zuwa babbar kotu.

Leave a Reply