Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya bayyana cewa za a sake fasalin kuɗin Naira 200 da 500 da kuma 1000.
Ga wasu abubuwan da ya kamata ku sani game da sake fasalin Naira;
1.Sabbin takardun N200, N500 da N1000 da aka sake fasalin za su fito ne a ranar
15 ga Disamba, 2022.
2.Tsofaffin kuɗaɗe za su ci gaba da gudana za kuma a cigaba da amfani da su har zuwa ranar 31 ga Janairu, 2023 bayan haka, doka ta hau kansu, za a daina karɓa.
- Duk me ajiyeyyen takardun na N200, N500 da N1000 ya maidasu zuwa banki, za a tura masa ta asusun ajiyarsa na banki.
- A wannan lokacin canjin kuɗin, CBN ta daƙatar da cajin duk wasu kuɗaɗen da ake yi akan kuɗin ajiya a wannan lokacin.
- Ana sa ran bankunan za su ƙara wa’adin kwanakin da suke aiki a cikin mako domin baiwa jama’a damar ajiyar kuɗaɗen hannunsu.