Alherin janye tallafin manfetur, daga Auwal Mustapha Imam PhD

3
237

Shi fa wannan lamari na janye tallafin da gwamnati ta yi a man fetur gabaɗayansa alheri ne ga talaka da Nigeria. Akwai raɗaɗi dai kafin a saba, amma idan an daure za a ga alherinsa. An daɗe ana siyasantar da lamarin cigaban Nigeria ne, shiyasa muka kasa gane tsare-tsaren da za su anfanemu da waɗanda za su cutar da mu.

Tun a lokacin mulkin Obasanjo aka so a cire tallafin man fetur, amma siyasa ta hana. An yi ta tallace-tallace a gidajen TV da radio don a wayar da kan talaka cewa “deregulation” a fannin man fetur shine mafita ga cigaban ƙasa Nigeria, amma an kasa aiwatarwa. Kowa tunaninsa idan ya aiwatar, ba lallai jam’iyyarsa ta ci zaɓe ba.

Gwamnati na kashe tiriliyoyin kuɗi wurin biyan tallafin man fetur da ake shigowa da shi domin a ɗauki man fetur ɗin a sauke a ko ina a Nigeria cikin sauƙi. To amma hakan ba mafita bane, domin kuɗin da ya kamata a yi wa Nigeria ayyukan cigaba su ne ake kashewa wurin biyan tallafin.

Jiya na ce, na samu ƙarin sama da Naira dubu ashirin (N20,000) a kan yadda na saba sayen mai. Kenan a duk lokacin da na saya man fetur, gwamnati na yi min cikon kuɗi. Motoci na guda biyu ne, kuma aƙalla na kan cika tankin kowace sau biyu a wata ɗaya. Kenan gwamnati na yi min cikon sama da Naira dubu ɗari a kowane wata. Abin tambaya shine, shin wanda bashi da mota shi ta ina gwamnati ke taimakonsa?

KU KUMA KARANTA: Cire tallafin mai: An tashi baran-baran tsakanin ƙungiyar ƙwadago da Gwamnatin Najeriya

Za ku iya cewa idan man fetur yayi sauƙi, talaka zai samu sauƙin kayan masarufi, to ai ni ma da kuma duk wanda ke da mota muna samun wannan sauƙin na kayan masarufi. Hanya ɗaya da gwamnati za ta samar da anfanuwa ga kowa shine a samar da hanyoyin sufuri masu inganci ga kowa, a samar da asibitoci da magunguna, a samar da makarantun boko masu kyau da Malamai masu nagarta. Duka waɗannnan ba za su samu ba, saboda babu wadatattun kuɗaɗe da za a yi haka.

Kuɗaɗen da ya kamata a samar da su, sune suke tafiya wurin biyan tallafin man fetur. Idan kun lura, man fetur ya fi tsada a duka sauran ƙasashen duniya da suka cigaba. Suna anfani da kuɗaɗen su wurin samar da cigaban ƙasa. Amma a Nigeria, ana karkatar da kuɗaɗen wurin biyan tallafin man fetur.

A baya, gwamnatin shugaba Jonathan ta rage tallafin, sai ta ƙirƙiro hukumar SURE-P da ta yi anfani da waɗannan kuɗaɗen da aka rage na tallafin domin aiwatar da ayyukan cigaban ƙasa da samar da walwala ga yan ƙasa. Tun a shekarar da ta gabata shugaba Buhari ya sanar da janye tallafin gaba ɗaya, sai koke-koke yayi yawa na matsanancin hali da ake ciki. Daga nan ne sukayi alƙawarin janye tallafin gaba ɗaya a watan June ɗinnan da muke ciki.

A taƙaice, duk da cewa Shugaba Tinubu na da niyyar cire tallafin gaba ɗaya idan ya amsa mulki kamar yadda ya sanar tun kafin ya ci zaɓe, amma ya zo ya tarar da kammalallen shirin na cire tallafin a wannan watan. Shiyasa ya jaddada shi.

Wani abu kuma da ya kamata mu sani shine, dilolin man fetur na anfani ne da wannan tallafin wurin cin amanar ƙasa Nigeria. Suna shigo da man fetur su nuna wa gwamnati, idan aka biya su kuɗin tallafin, sai su karkatar da man zuwa gidajen mai masu tsada. Kenan dakatar da tallafin mataki ne na hana almundahana a Nigeria.

Samun sauyin rayuwa na da zafi, amma idan an daure, za a ga anfaninsa. Musamman idan an gudanar da gwamnati da gaskiya da amana.

Daga ƙarshe, ina bada shawara kamar haka;

  1. A rage zirga zirgan da ba su zama dole ba.
  2. A ririta kuɗi ta hanyar kaucewa abubuwan da basu da muhimmanci.
  3. Idan za ku yi tafiya da motocinku, ku tsaya ku ɗauki passengers a tasha domin a rage kuɗin mai. Amma a kiyaye da ɗaukar ɓarayi.
  4. A riƙa tafiya a ƙasa zuwa inda ba zai gagara ba.

Idan muka ɗauki waɗannan matakan, za mu samu sauƙi sosai kafin mu saba.

Muna roƙon Allah ya bamu abin saya. Amin.

Auwal Mustapha Imam , Ph.D.

3 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here