Yan sanda za su sake fasalin tsaro a babbar hanyar Legas zuwa Ibadan

1
277

Sakamakon karin bayanai kan yanayin tsaro dangane da babbar hanyar Legas zuwa Ibadan da kwamishinonin ‘yan sanda masu kula da jihohin Legas, Ogun, da Oyo suka isar wa babban sufeton ‘yan sandan Najeriya (IGP), Usman Alkali Baba, sufeton janar ya bayar da umarnin a sake yin gyare gyare cikin gaggawa domin sauya fasalin tsaro a kan babbar hanyar tare da sanya isassun jami’ai tare da kayan aikinsu don tabbatar da kare rayuka da dukiyoyi al’umma dake kai komo a kan hanyar tare da dakile sace-sacen mutane da sauran munanan abubuwan da ke faruwa a hanyar.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar’yan sandan Najeriya CSP Olumuyiwa Adejobi wanda ya aike wa kafar yaɗa labarai ta Neptune Prime.

Hakazalika, IGP Usman Alkali Baban ya jaddada cewa hukumar ‘yan sanda ta damu da ƙalubalen tsaro da ake fama da shi a kan babbar hanyar, sai dai ta himmatu wajen tsara hanyoyin da za a bi don daƙile matsalar tsaro da kuma kawar da baraza a kan hanyar, ta yadda za a iya magance matsalar.

Don haka Sufeto-Janar na ‘yan sandan ya yi alƙawarin bayar da cikakken goyon bayan gudanar da aiki ta hanyar fasahar zamani da ƙere-ƙere tare da samar da kayan aiki ga kwamishinonin ‘yan sandan da ke kula da jihohin Legas, Ogun, da Oyo, da kuma shugabannin rundunonin gudanar da dabarun yaƙi a yankin domin yaƙar halin da ake ciki na laifuka da ɓata gari ke aikatawa a kan babbar hanyar ta Legas zuwa Ibadan.

Hakazalika, Sufeto Janar na ‘yan sandan ya yi kira ga ‘yan Nijeriya masu kishin ƙasa, musamman masu amfani da hanyoyin da mafarauta da shugabannin al’umma, da sauran masu ruwa da tsaki da ke bin wannan hanya da su riƙa tona asirin ɓarayin da ke addabar ‘yan Nijeriya da ba su ji ba ba su gani ba a kan hanyar, inda yayi kiran ga kuma maƙwabtan hanyar da al’umma da ke zaune a yankin da su dinga bai wa ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro bayanai domin kama ɓatagarin tare da gurfanar da su cikin gaggawa.

1 COMMENT

Leave a Reply