‘Yar shekara 10 ta lashe gasar haɗa baƙi ta ‘Spelling Bee’ a Borno

2
601

Wata yarinya ‘yar shekara 10 mai suna Aisha Modu-Mustapha daga makarantar firamare ta Sanda Kyarimi ta lashe gasar haɗa baƙin boko ta ‘Spelling Bee’ ta shekara-shekara da gidauniyar Inara ke gabatarwa a Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Matashiyar Aisha ta rubuta kalmomin Whirligig, Quarreling, Administration, Willingly, Spaceless, Peasant da sauran su, har ta doke abokan hamayyarta Muhammad Muhammad-Dawule, daga makarantar Gamboru Primary School, da Bukar Muhammad daga makarantar Ibrahim Damchida.

Gidauniyar ta bai wa waɗanda suka yi nasara a gasar kwamfyutocin tafi-da-gidanka, kyautar tsabar kuɗi da kuma kayan karatu na maƙudan kuɗi.

Da take jawabi bayan kammala gasar a ranar Alhamis, wacce ta kafa gidauniyar Aisha Waziri-Umar, ta ce an shirya gasar ne domin tallafawa da kawo sauyi ga ilimi a jihar Borno.

Mai ba da agajin ta ƙara da cewa alfanun da ake samu ya wuce ƙwarewa a harshe hakan na taimaka wa yara wajen samun ƙwarin gwiwa da fahimtar juna da fahimtar jama’a, da kuma samun nutsuwar yin abinda duk ake buƙata a yanayi na matsin lamba.

Shima, da yake nasa jawabin Manajan shirin na gidauniyar Inara, Usman Umar-Dagona, ya bayyana cewa gidauniyar wata ƙungiya ce mai zaman kanta, wacce take tallafawa ilimi, ƙirkire-ƙirkire da kuma marasa galihu a Najeriya, musamman a Arewa maso Gabas ta hanyoyi daban-daban na ayyukan al’umma.

A kwanakin baya ne gidauniyar ta ƙaddamar da cibiyarta ta farko ta Codeing, Robotics da kuma Programming a yankin Arewa maso Gabas a Maiduguri, inda aka horas da matasa 30 sana’o’i daban-daban na fasahar zamani da suka haɗarda fasahar ƙira mutum-mutumi da codeing.

2 COMMENTS

Leave a Reply