Shugaba Buhari ya karrama ɗan Daudu, Ɗan luwaɗi

A farkon wannan satin ne, 11 ga watan Oktobar 2022, shugaban Najeiya Muhammadu Buhari ya jagoranci bikin karrama ƴan ƙasa waɗanda suka bawa al’umma gudummawa a matakai daban-daban na rayuwa, Sai dai taron ya bar baya da ƙura.

Mr Ezra Olubi

Kazalika, Ƴan Najeriya da dama a kafofin sadarwa zamani suna ta tofa albarkacin bakin su yayin da aka hango wani fitaccen ɗan ƙungiyar ƴan Luwadi Mr. EZRA OLUBI a cikin waɗanda aka karrama da lambar yabon ta OON (Order Of The Niger).

Yayin da shugaba Buhari ya saki baki yana kallon Ezra

Abin lura: Ga duk wanda ya kalli bidiyon an gano shi kansa shugaba Buhari ya saki baki yana kallon yanayin shigar Olubi wanda ciki harda bakin jan-baki ya goga a laɓɓansa sa da wannan shigar kayan da ya yi.

Babban abun tambayar shi ne shugaban ƙasa ne yake zaɓo mutane? Ko kuma wasu ne suke zaɓo fitattun mutanan domin a karrama su? idan haka ne menene ribar su na zaɓo irin su Ezra ko dai suna da alaƙa ne?


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *