An samu harsashi fiye da 12 a jikin Thomas Sankara

0
334

Harsasai (bullets) fiye da goma sha biyu aka samu a jikin shugaba Thomas Isidore Noel Sankara, lokacin mutuwar sa.

A rana irin ta yau 15 October ta shekarar 1987 aka kashe shugaban ƙasar Burkina faso mai suna Thomas Sankara. Sankara shine ya sauyawa ƙasarsa suna daga French colonial upper volta izuwa Burkina faso.

An kashe shi a sanadiyyar juyin mulki (coup) wanda babban abokinsa ne ya tsara komai, ya mutu yana matashi ɗan shekaru 37 kacal a duniya.

Kasancewarsa jajirtacce kuma mai tsananin ƙiyayya ga zalunci, da azzalumai, rayuwarsa abar koyi ce, matasa da dama a duniya sun ɗauke shi a matsayin allon kwaikwayo.

Leave a Reply