Meye ra’ayinka kan mauludi? Tattaunawarmu da wani a kan Mauludi, Daga Yusuf Alhaji Lawan

Na fito da safe zan raka yara makarantar Islamiyya a wata ranar Asabar, isar mu bakin makarantar ke da wuya, sai ga abokina shima ya kawo nasa yaran. Bayan sun shiga sai ni dashi muka kamo hanyar komawa gidajenmu.

To wannan ranar tayi dai-dai da 12 ga watan Rabi’ul Auwal. Sai muka ci karo da yara ‘yan Islamiyyoyi da kayan makaranta wasu da shiga kala-kala zasu tafi wajen zagayen Mauludi. Cikin wasa sai nacewa abokina, kaga muma da munyi sabbin dinki iri ɗaya ai da munje riyadar mauludin nan, yace gaskiya fa.

Da muka cigaba da tafiya, sai yace mun wane, mu ajiye maganar wasa a gefe, don Allah meye ra’ayinka a kan mauludi? Sai na kada baki nace masa ai ni bani da matsala da mauludi. Sai yace mun to shi yana da matsala da mauludi. Nace masa to ina sauraronka. Sai ya ƙara da cewa akwai Hadisin Annabi da yace duk wadda ya ƙirkiro wani abu a cikin addini to ba’a karba ba. Da wannan dalilin ne yasa shi baya tare da mauludi.

Nace masa to wane ni yanzu ba zan baka wata hujja ta yin mauludi ba, amma zan faɗa maka wasu abubuwa irin mauludi da suma aka ƙirkiro su da zaka taya ni neman hujjojinsu. Idan ka samo, to sai mu dawo kan mauludi. Yace mun yana saurarena.

Ban san ko ka taba halartar tafsirin Al-Qur’ani mai Girma a cikin watan Ramadana ba. Yace sosai yana halarta. Nace masa to a Makka ko Madina Annabi ya fara tafsirin Al-Qur’ani a Ramadan? A shekara ta nawa kafin hijira ko bayan hijira ya fara? Cikin sahabbai waye mai ja masa baki? Bayan Sallar Asuba yake yi ko da hantsi? Da yamma ko da dare? Maza da mata yake yiwa a hade ko kowa daban yake musu nasu? Idan yayi fashin fitowa waye yake gabatarwa a madadinsa?

Sai gasar karatun Al-Qur’ani. Ita kuma a wace shekara Annabi ya fara shiryawa? Cikin sahabbai waye yake zama zakara? Wadanne kyaututtuka yake rabawa ga wadanda suka yi fice? Ruwayoyin Qira’a nawa aka yi amfani dasu? Su waye manyan alƙalan gasar?

Sanya sunayen sahabbai ko wasu bayin Allah na gari ga masallatai. Shi Annabi wane suna ya sanyawa nasa masallacin? Sannan a tarihin rayuwarsa masallatai nawa ya sawa suna? Sannan menene misalsalai na irin sunayen da yayi ta sakawa masallatai?

Sallar Tahajjud jam’i a masallatai da azumi. Ruwayoyi nawa aka samu da suka zo da yadda Annabi yake gudanar da sallar Tahajjud jam’i a masallacinsa? A wace shekara ya fara? Da kira’ar Hafsi, Warshi, Tangimi, Duri ko Susi yake karatu? Sannan kowace raka’a sumuni ko rubu’i ko izu yake karantawa? Sannan saukar Qur’ani yake yi cikekke ko wasu izu yake karantawa? Idan akwai ranar da bai samu fitowa ba, cikin sahabbai waye yake gabatarwa a madadinsa? Shi kadai yake yin limancin ko suna yin karba-karba da wani ko wasu daga sahabbai?

Sallar Tarawihi jam’i a masallatai. Malamai sun faɗa mana cewa tunda Annabi yayi sau 2 a masallaci mutane suka bishi bai sake yi ba, yace ina tsoron a wajabta muku kuma ba zaku iya ba, sai ya koma gida yana yi shi kadai, kuma har ya bar duniya ba’a kara yin sallar Tarawihi jam’i a masallacin Annabi ba. Har Sayyidina Abubakar ya gama halifancinsa ba’a yi Tarawihi jam’i ba. To da wane dalili aka jingina yanzu ake yin sallar Tarawihi jam’i a masallatai?

Kafa kwamitin masallaci kuma sunnar waye? A zamanin Annabi waye ciyaman din masallacin Annabi? Waye ma’aji? Waye magatakarda? Waye jami’in hulda da jama’a na masallacin Annabi?

To wa’azin ƙasa fa? Wa’azin jiha dana karamar hukuma? Idan Annabi ne yayi, to a shekarar daya fara su nawa ne suka gabatar da muhadara a wajen? Alarammomi nawa ne masu jan baki ga Malamai da suka gabatar? A wane gari Annabi ya fara?

To dama wasu ire-iren waɗannan da lokaci ba zai bani damar gama kirga maka su ba, ina son ka taya ni nemo hujjojinsu a Qur’ani ko Hadisan Annabi. Idan ka samu to sai nima na nemo maka hujjar mauludi.

To amma ina mai tabbatar maka cewa zaka sha wahalar nema kuma da wahala ka iya samo hujja ta kai tsaye akan duk waɗannan tambayoyi sai dai tawili. To kuma duk wata hujja da zaka samar ta tawili to mai mauludi ma zai hau kai. Idan kace ana yin gasar karatun Al-Qur’ani ne saboda a sanya son Qur’ani a zuƙatan musulmi ko don a ƙarfafa koyonsa, mai mauludi ma zai ce maka ai wannan shine dalilin mauludi kuma shi yasa ake karatun Al-Qur’ani a wajen. Idan kace sanya sunan sahabbai ko bayin Allah na gari a masallatai aikin kirki ne, to mai mauludi ma zai ce maka shima Mauludi aikin kirki ne da kuma sauran dalilai irin wadannan.

Idan ka gamsu cewa yin tafsirin Al-Qur’ani a Ramadan, Sallar Tahajjud jam’i, Gasar karatun Al-Qur’ani da sauransu duk basu da hujja ta kai tsaye daga Annabi to amma kai sun maka, kuma zaka yi su, to sai ka yarda cewa yadda kake da ‘yancin yin su, haka mai yin mauludi ma yana da irin wannan ‘yancin.

Idan kuma ba haka ba, to sai mu hada kai mu watsar da dukkan wadannan abubuwan har ma da wadanda ban ambata ba tunda Annabi bai yi su ba.

Sai abokina yayi shiru na wani ɗan lokaci sai yace mun to yaya aka yi malaminsu bai san duk wadannan bayanan da nayi ba? Nace masa ya sani mana, kawai ba zai fada muku bane tunda shi yana da tasa manufar. Sai yace mun wallahi malaminsu bai san duk wadannan ba kuma sai yaje ya same shi ya fada masa.

Bayan mun gama tattaunawa, sai muka rabu kowa ya wuce gida. To yanzu ina saurare naga ko zai dawo ya fada mun yadda suka yi da Malaminsa ko a’a. Zai sassauta ya daina fada da mauludi ko zai fara yin mauludi shima. Zai kaikasa kasa ya cigaba da sukar mauludin ko zai yi shiru.

Allah ya ƙara mana soyayyar Ma’aiki s.a.w, ya sanya mu cikin cetonsa. Allah ya haskaka zuƙatan musulmi su fahimci daɗin soyayyar Annabi Muhammadu s.a.w.


Comments

2 responses to “Meye ra’ayinka kan mauludi? Tattaunawarmu da wani a kan Mauludi, Daga Yusuf Alhaji Lawan”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Meye ra’ayinka kan mauludi? Tattaunawarmu da wani a kan Mauludi, Daga Yusuf Alhaji Lawan […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: Meye ra’ayinka kan mauludi? Tattaunawarmu da wani a kan Mauludi, Daga Yusuf Alhaji Lawan […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *