Yan-sanda sun ceto mata tara da za a yi safararsu zuwa Libya a Jihar Katsina

0
246

‘Yan-sanda sun ce sun yi nasarar ceto wasu mata tara da suka fito daga wasu jihohin Najeriya daban-daban da ake shirin safararsu zuwa ƙasar Libya, a ranar Laraba. Kakakin rundunar ‘yan-sandan JIhar Katsina, SP Gambo Isah, wanda ya bayyana haka, ya ce sakamakon bayanan sirri da suka samu ne jami’ansu suka yi wa wata maboya ta masu safarar dirar-mikiya a yankin ƙaramar hukumar Daura inda suka ceto matan.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, kakakin ya yi bayani kan matan inda ya ce, ”waɗanda aka ceto su ne Timilaye Ojo mai shekara 26 daga Jihar Lagos da Blessing Joseph mai shekara 19 daga Jihar Edo da kuma Khadija Abdullahi mai shekara daga Jihar Ondo. “Haka kuma akwai Safiyyat Ahmed mai shekara 21 daga Jihar Lagos da Precious Nuhu mai shekara 22 daga Jihar Kaduna da kuma Bolanle Adewusi mai shekara 32 daga Jihar Ogun,” in ji shi.

Kakakin ya ce “Sauran su ne Okpoekwu Eunice mai shekara 28 daga Jihar Enugu da Kabirat Azeez mai shekara 19 daga Jihar Ondo da kuma Taiwo Adeolo mai shekara 27 daga Jihar Ondo”. Mai magana da yawun ‘yan-sandan ya ce, a yayin binciken da suka yi sun gano cewa an ɗauko matan daga Jihar Kano ne zuwa Daura a jihar Katsina, a mota, wadda direban ya gudu ya bar matan bayan da ya ga ‘yan-sanda.

Ya ƙara da cewa za a kai su ƙasar Libya ne ta Nijar, kafin a ceto su, tare kuma da bayar da tabbacin cewa za a kamo masu safarar kasancewar ana ci gaba da gudanar da bincike.

Leave a Reply