Hukumar zaɓen Najeriya INEC ta bayyana cewa dole jam’iyyun ƙasa da aka yi wa rajista su bayyana inda suka samu kuɗin kamfen ɗinsu da kuma bin ƙa’idojin da aka gindaya na kashe kuɗi a lokacin yaƙin neman zaɓe.
Shugaban na INEC Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a yayin wata hira da gidan talabijin na Trust TV a Najeriya, inda ya ce akwai kuma adadin da aka ƙayyade na irin gudunmawar kuɗi da mutum zai iya bai wa jam’iyya a yaƙin neman zaɓe.
Haka kuma ya ƙara jaddada cewa jam’iyyu ba za su iya karɓar tallafin kuɗi ba daga ƙasashen waje.
A cewarsa, idan ma an samu irin wannan tallafin, ya zama dole a tura wa hukumar zaɓe waɗannan kuɗaɗe.
[…] Previous articleKada jam’iyyu su kuskura su karɓi tallafin kuɗi daga ƙasashen waje – INEC […]
[…] KU KUMA KARANTA: Kada jam’iyyu su kuskura su karɓi tallafin kuɗi daga ƙasashen waje – INEC […]