Asirin wani sojan gona ya tonu a jihar Kano

Daga Shafaatu DAUDA, Kano

Rundunar hukumar kare rayuka da dukiyoyin Al umma ta jihar kano (civil defense) tayi nasarar kame Wani matashi Mai suna Umar A Alasan Mai shekara 31 a ƙaramar hukumar kumbotso.

Matsahin dai ansame shi da wayoyin salula, da kayan jamian tsaro na civil defense ɗauke da number aiki gamida ID card na hukumar.

Ƙunshin kayayyakin da aka samu a hannun wanda ake zargi da amfani da kayan rundunar tsaro ta civil defense dake kano

Jami in hulda da jama’a na hukumar ta civil defense ya tabbatar da faruwar lamarin, DSC ibrahim saminu Abdullahi, yace sun sami nasara ne tareda tallafin jami’an tsaro na ‘yansanda. Ya ƙara da cewa yazama wajibi suyi godiya da Al umma bisa yadda suke bawa wannan rundunar haɗin kai wajan Basu labarai na gaskiya.

Matsahin ya amsa lefinsa har ya roƙi da ayi masa afuwa. A nasa ɓangaren, mai magana da yawun hukumar yace dazarar sun kammala bincike zasu GURFANAR dashi a kotu don yimasa hukuncin da ya dace dashi.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *