Yadda ‘yan sanda suka ceci wasu mutane 7 da ake daf da binne su da ransu a Jigawa

0
252

Rundunar yan sandan Najeriya reshen Jihar Jigawa ta hana mutanen gari a karamar hukumar Birniwa birne wasu mutum bakwai da ransu, The Nation ta rahoto.

Da rabon wasu mutane bakwai a garin Bursali za su cigaba da shaƙar iskar rayuwa, bayan da gini ya rufta musu ya danne su kuma mutanen gari suka ceto su amma ba su numfashi.

Mutanen gari sun shirya tsaf za su binne mutanen bakwai da aka ciro su ba su numfashi daga baraguzan ginin, amma ‘yan sanda suka ce dole a kai asibiti a tabbatar.

Cewa a kai mutanen asibiti a tabbatar da mutuwarsu ya janyo zazzafan jayayya tsakanin ‘yan sanda da ‘yan uwansu amma daga ƙarshe ‘yan sanda suka yi nasara kuma da zuwa asibit likita ya ce dukkansu bakwai suna da rai.

Mutanen kauyen sun ceto waɗanda abin ya faru da su kuma suna shirin musu jana’iza. Kakakin yan sandan Jihar Jigawa DSP Lawal Shiisu Adam ya ce: “Wani ginin ƙasa a Bursali ya rufta kan wasu mutane bakwai suka makale. “Da samun labarin, an tura tawagar ‘yan sanda zuwa wurin da abin ya faru.

Da isarsu, sun ga mutum bakwai ba su numfashi da guda daya wanda ya jikkata sosai.” DSP Shiisu ya ce mutanen garin sun fara shirin birne waɗanda aka ciro ba su numfashi yayin da ‘yan sanda suka dage sai an kai su asibiti an tabbatar.

‘Yan sandan sun dage cewa sai an tafi asibiti an tabbatar. Bayan jayayya mai zafi, yan sandan suka yi nasara aka kai su babban asibitin Birniwa. Da isarsu asibitin, likita ya duba su ya ce dukkan mutanen bakwai da aka ce sun mutu suna da rai. “Har ta kai ga huɗu daga cikinsu sun fara iya magana a asibitin.

Sanawar da kakakin ‘yan sandan ya fitar ta yi kira ga mutane su riƙa ƙyale jami’an tsaro su yi aikin da doka ta dora musu.

Leave a Reply