Kisan Ummita: Al’ummar China sun yi Allah-wadai da kashe Ummu Khulthum Buhari

1
310

Ƙungiyar ‘yan kasuwan ƙasar Sin ta Najeriya (CBCAN) ƙarƙashin jagorancin Wakilin Mutanen China ‘yan Kano, Mista Mike Zhang, ta yi Allah-wadai da kisan wata Ummulkulthum Buhari da wani ɗan ƙasar China, masoyinta Geng Quanrong ya yi.

KU KUMA KARANTA: Wani bincike da aka gudanar akan makashin Ummita

A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu a madadin Wakili ta hannun mataimakinsa na musamman, Mista Guang Lei, Zhang, ya ce wannan mataki da Geng ya ɗauka abin la’anci ne, kuma wannan laifi ne da ya kamata hukumomin tsaro da masu ƙwarewa a harkar su ɗau mataki.

A cewar sanarwar “Al’ummar Sinawa mazauna Kano, suna goyon bayan doka tayi duk abinda ya kamata. Har ila yau, sun yaba da irin karramawar da aka yi wa yan al’ummar Sinawa mazauna Kano, kuma za su ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda, da sada zumunci, da kuma ba da gudummawa ga ci gaban Kano.

A cikin sanarwar, al’umma ta mika ta’aziyya ga iyalan marigayiyar Ummukhulthum Buhari.

1 COMMENT

Leave a Reply