Wani bincike da aka gudanar akan makashin Ummita

1
374

A ci gaba da afkuwar lamarin da ya kai ga rasuwar Ummah, manema labarai sun gana da DPO na Ɗorayi Baba a Asibitin UMC, domin miƙa gawar zuwa asibitin gwamnati, domin ba da takardun da suka dace don binne gawar a gaba.

Daga nan ne suka tafi tare domin yi wa dan ƙasar Sin da ya aikata laifin tambayoyi. An samo bayanai kamar haka:

Suna: Geng Quanrong
Ƙasa: Sinanci
Shekaru: 47 shekaru
Lambar fasfo: E56374165
Sunan kamfani: Kamfanin BBY Textile a Kasuwar Kwari hanyar Unity Road.
Sunan Ma’aikaci: Auwal Sanusi Aminu
Lambar wayar masu daukan ma’aikata: 08033493770

A cewar wanda ake tuhumar, ya ce shekara 2 da suka gabata suna soyayya, ya kashe makudan miliyoyin naira ga yarinyar da danginta, sai dai yarinyar ta daina ɗaukan kiransa. Ya ce kishi da takaicin yadda yarinyar ta yi watsi da shi ne ya sa ya daba mata wuƙa.

KU KUMA KARANTA: Dan ƙasar China ya kashe budurwarsa ‘yar Kano

A cewar ma’aikacin, ya ce Geng CERPAC Izinin zamansa ya ƙare, ya baiwa jami’in shige da fice a MAKIA daya taimaka masa ya sabunta.

Geng ya ce ya saba amfani da kayan masaƙa daga ƙasar China zuwa Najeriya, sannan ya miƙa su ga mai aikin sa don taimaka masa wajen siyar da su a kasuwar Kwari

A halin yanzu ma’aikacin ya yi ikirarin yana ƙasar Turkiyya, cewa bai san lokacin da zai dawo Najeriya ba.

Geng yana da mata ‘yar shekara 46 a kasar Sin da ‘ya ‘yar shekara 13 duk a ƙasar Sin.

Fassarawa: Comrd Ibrahim Da’u Dayi

1 COMMENT

Leave a Reply