Amurka na neman wani ɗan Najeriya da ya damfareta dala miliyan talatin 30

1
763

Daga Fatima MONJA, Abuja

Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka FBI, na neman wani ɗan ƙabilar Igbo a Nageriya bayan ya damfari gwammatin New York kuɗaɗen da suka haura dala miliyan talatin 30, wanda yayi dai dai da biliyan 15 na kuɗin Nageriya.

Wata sanarwa da Ofishin babban lauyan gwamnati Amurka ta fitar tace ana tuhumar Chidozi Collins Obasi mai shekaru 29 kan aikata laifuka da dama da suka haɗa da damfara ta hanyan amfani da saƙwanni ta yanar gizo.

A farkon ɓarkewar annobar korona Obasi yayi ta sayarwa asibitocin da cibiyoyin kiwon lafiya na Amurka na’urar numfashi na boge, kafin daga bisani ya saci bayanan wani ba’amurike, inda yayi ta karɓan kuɗaɗen rage raɗaɗin annobar Korona.

Hukumar Amurka tace ba Obasi ne kaɗai ke aikin damfarar ba, domin kuwa yana da wasu mataimaka a Ƙasar Kanada, amma daga Nageriya shi yake nashi ayyukan damfarar.

Muddin dai FBI tai nasarar cafke shi, Obasi ka iya fuskantan hukuncin zama a gidan kaso na sheraru 621 da kuma tarar dala miliyan 5 da dubu 750.

Kazalika hukumar ta Amurka zata tilasta mishi dawo da duk kuɗaɗen da ya sace wanda suka haura dala miliyan 30 kamar yadda jaridan RFI ta rubuta.

1 COMMENT

Leave a Reply