Arangama tsakanin ISWAP da Boko Haram tayi sanadin mutuwar mahara

0
297

An yi wata arangama tsakanin ƙungiyar Boko Haram ɓangaren Abubakar Shekau da tsagen ƙungiyar ƙarƙashin ISWAP, a arewa maso gabashin Najeriya, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar wani babban kwamandan kungiyar mai suna Kundu.

Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne tsakanin Dikwa da Bama da ke jihar Borno.

Wata majiyar tsaro ta ce Kwamanda Kundu tare da tawagarsa na kan aikata fashi da makami, lokacin da mayaƙan ISWAP din a kan babura shida, kowanne ɗauke da mutum uku suka far musu.

A baya-bayan nan dai ana yawan samun arangama da juna tsakanin ƙungiyoyin da a baya suka addabi al’umar ƙasar.

Leave a Reply