Fashin baƙi kan batun ƙirkiro ‘yan sandan jihohi a Najeriya – Barista Bulama Bukarti

1
807

Masana harkokin tsaro a Najeriya su ce akwai fargaba kan batun neman kirkiro ‘yan sandan jihohi lura da yadda lamura ke tafiya da kuma tarin kalubale ko matsaloli da ka iya biyo baya.

Masanan suna wannan tsokaci ne bayan da kungiyar gwamnonin arewacin kasar da kuma majalisar sarakuna suka yi kiran da a samar da ‘yan sandan jiha, domin taimakawa wajen tunkarar matsalar tsaron da ake fuskanta a yankin.

Kafin wannan lokaci, jihohin kudancin kasar ne ke kan gaba wajen fafutukar ganin an samar da ‘yan sandan jiha, yayin da jihohin arewacin Najeriyar ba sa goyon bayan hakan.

Sai dai bayan kammala wani taro da gwamnonin arewan suka yi a farkon makon nan, sun nuna bukatar a samar da ‘yan sandan a matakin jiha al’amarin da masana ke ganin na tattare da fargaba.

Barista Bulama Bukarti babban jami’i ne a cibiyar kawo sauyi a kasashen duniya ta, Tony Blair da ke London, ya ce duk da cewa halin tabarbarewar tsaron kasar ne ya bar shugabannin arewa cikin yanayi na rashin zabi akwai abin dubawa sosai.

Bulama Bukarti ya ce babu shaka an jima ana wannan kiraye-kiraye, amma da ya ke yanzu tura ta kai bango, kusan babu zabi ne a yanzu.

Ya ce kirkiro ‘yan sanda ba wai abu ne mai wahala ba, kawai zaman gyara kudin tsarin Mulki ne.

Sai dai a wannan yanayi abin zai kasance ne kamar gaba kura baya sayaki, saboda idan aka yi duba kusan duk abubuwan da kudin tsarin Mulki ya bai wa gwamnoni, harkokin ba wai sun inganta ba ne ko sun zarta na gwamnatin tarayya.

Ya bada misali da asibitocin jihohi, da makarantu da sauran abubuwan da kudin tsarin Mulki ya bai wa gwamnoni damar samarwa amma abubuwa ba su inganta ba.

Wannan dalili ya sanya Bulama Bukarti ke ganin koda an bai wa jihohi damar kirkirar ta su rundunar ‘yan sanda ba lallai lamura su inganta.

‘’Ko kadan gwamnoni ba su nuna wata alamar za su iya tafiyar da harkokin da ke hannusu cikin aminci ba fiye da gwamntin Tarayya’’.

Bulama Bukarti na ganin akwai fargabar idan aka bai wa gwamnonin ‘yan sanda a hannusu, domin za su yi amfanin da damar wajen cusgunawa duk wadanda basa so musamman abokan hamayyar siyasa, a cewarsa.Ya bada misali da batun hukumomin zaɓe na jihohi, yana mai cewa tun da aka sakarwa gwamnoni harkar, kusan babu wani wuri da za a ce gashi an yi zabe mai inganci.

Ya kuma ce idan har ya zama dole a yi ‘yan sanda jiha to dole a fitar da dokar da za ta yi bayyani dalla-dalla kan huruminsu da kuma ‘yan sanda tarayya.‘’Sannan akwai bukatar dole a ware iyakoki jihohi dalla-dalla saboda kaucewa artabu tsakanin ‘yan sanda jihohin’’.

Masanin ya kuma ce dole makamansu ya kasance yana ƙarƙashin shugaban ƙasa ko gwamnatin tarayya, ta yada wani gwamna ba zai iya shigo da makaman da suka zarta kima ba, har a iya samun masu kokarin ballewa daga Najeriya.

1 COMMENT

Leave a Reply