Sojoji sun tarwatsa mayaƙan babban ɗan bindiga Boderi, shi kuma yasha da ƙyar

1
474

Daga Fatima GIMBA, Abuja

Shahararren ɗan fashin nan mai suna Boderi Isiya, ya tsallake rijiya da baya, yayin da dakarun sojojin Najeriya suka bindige babban kwamandan sa na biyu tare da wasu mayaƙa da dama.

Samuel Aruwan, kwamishinan ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida ta jihar Kaduna, ya bayyana cewa hukumomin tsaro sun sanar da gwamnatin jihar ci gaban da aka samu ta hanyar da ta dace.

A cewarsa, binciken da aka yi da wasu majiyoyi masu sahihanci na leƙen asirin ɗan adam ya ƙara tabbatar da cewa Boderi da ƙungiyarsu ta ‘yan ta’adda sun yi mummunar rana a hannun dakarun da ke shirye-shiryen yaƙi.

Ya ce, “Sojojin sun yi artabu da ‘yan bindigar a kewayen babban yankin Tollgate da ke karamar hukumar Chikun. ‘Yan ta’addan sun yi artabu da ja da baya, sai dai suka ci karo da wani harin kwantan ɓauna da sojojin suka yi a yankin Sabon Gida, inda suka fatattake su.

“An kwato gawawwaki da makamai a wurin, yayin da wasu daga cikin ‘yan ta’addan suka mutu a sakamakon raunukan harsasai.

“Mutumin Boderi na biyu, Musti, yana daga cikin waɗanda aka tantance, tare da Mai-Madrid Yellow ɗaya da Dan-Katsinawa ɗaya, da sauran waɗanda har yanzu ba a tantance ba. Wasu daga cikin ‘yan ta’addan na fafatawa da raunukan da ke barazana ga rayuwarsu,” inji shi.

Samuel Aruwan ya ce, Musti da Boderi ne ke da alhakin taɓarɓarewar tsaro a makarantar horas da sojoji ta Najeriya da ke Kaduna tare da yin garkuwa da ɗaliban Kwalejin Injiniya ta Tarayya da Sarkin Bungudu da wasu ‘yan ƙasa da dama a bara.

Kwamishinan ya ce gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya yaba wa sojojin bisa wannan gagarumin aiki da suka yi a ƙarƙashin jagorancin Janar Hafsan Soja ta daya, Manjo Janar T.A. Lagbaja, kasancewarsa na baya-bayan nan na manyan nasarorin da aka samu tun lokacin da ya hau mulki.

Aruwan ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar Kaduna za ta ci gaba da sanar da jama’a abubuwan da ke faruwa.

Ya yi kira ga ‘yan kasa da ke da bayanai masu amfani dangane da ‘yan fashin da aka ruwaito suna neman kulawar lafiya a yankin baki ɗaya da sauran wurare, da su kawo irin waɗannan bayanai ta lambobi kamar haka: 09034000060, 08170189999.

1 COMMENT

Leave a Reply