‘Yan bindiga sun kai farmaki babban Kamfani a Kaduna

0
393


Daga Saleh INUWA, Kano

Rahotanni daga jihar Kaduna na bayyana cewar wasu gungun ‘yan bindiga sun kai farmaki wani kamfanin gona a garin Anchau na ƙaramar hukumar Kubau dake jihar inda suka yi mummunan ta’adi.

Rahotannin sun bayyana cewar tsagerun ‘yan bindigar sun bindige wani soja har lahira tare da yin awon gaba da wasu jami’an kamfanin gonar mutum biyu da misalin karfe 1:30.

An tattaro cewa, ɗaya daga cikin waɗanda aka sacen wani ɗan ƙasar Zimbabwe ne da ke aiki a kamfanin. Wani ɗan banga da ke aiki a unguwar da abin ya faru ya ce sunan ɗan ƙasar Zimbabwe ɗin da aka sace Mista Charles Choko.

A cewarsa: Sun kashe wani soja da ke aiki a kamfanin na gona tare da yin awon gaba da wani mutumi mai suna Charles Choko ɗan Ƙasar Zimbabwe, da wani Yusuf Aliyu Bello dan jihar Kano.

Wani mutumin ƙauyen da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida cewa, ya ga tawagar jami’an tsaro a ranar Juma’a tana shiga dajin da ke yankin, domin nemo waɗanda aka sacen.

An kira shugaban ƙaramar hukumar, Basher Suleiman Zuntu, amma ba a same shi ta waya ba. Haka nan, bai mayar da sakon tes da aka tura masa ba.

Leave a Reply