‘Yan bindiga sun datse wa manomi hannayensa a Zamfara

0
296

Wani manomi a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya, mai suna Malam Sama’ila Muhammad, wanda ƴan bindiga suka datse wa hannayensa biyu ya ce ya miƙa lamarinsa ga Allah kuma shi ne kaɗai zai saka masa.

Manomin da ke zaune a ƙauyen Walu a ƙaramar hukumar Kauran Namoda ya bayyana cewa shi da ƴan uwansa sun ci karo da ƴan bindigan ne bayan sun fatattaki wasu ɓarayi da suka je satar kaji a gidansu kusan sha biyun dare, fiye da mako guda da ya wuce.

Malam Sama’ila ya shaida wa BBC cewa “bayin Allah ne suka shiga gidanmu, suka kama kaji sai suka fita, sai na ji sun shiga wajen ƙanina suna bugunsa, sai na ce jama’a kun ji suna bugun auta, ku taho mu je gare su,”

“Ashe sun ji, sai suka tsallaka katanga suka fita da gudu, sai muka bi su, da muka bi su sun yi nisa sai nake cewa ƙannena su dawo tun da sun tafi su dawo, ashe waɗannan masu bindiga sun koro bisashe (dabbobi).”

Leave a Reply