Mahukunta ku gaggauta hukunta Sojojin da suka kashe Ustaz Goni Aisami, tare da biyan iyalansa diyya – Barista Bulama.

0
264

Daga Shafa’atu DAUDA, Kano

Fittaccen lauyan nan mai yaƙin kare haƙƙin bil adama dake Najeriya, Barista Audu Bulama Bukarti, ya bayyana mutuwar Shekh Goni Aisami, a matsayin babban rashi ga al-ummar jahar Yobe, dama ƙasa baki daya.

Bukarti ya bayyana hakan ne a shafin sa na Facebook, inda yace Malamin bashi da aiki sai wa’azi da kira ga al-ummah cewa abi Allah. Malami ne wanda baya tsoron tsage gaskiya ko ya sayata ko akan wanene.

Bukarti ya ƙara da cewar, ba abin da ya dami Mallamin sai abinda ya dami al-ummah. Inda yace ko wayar da su kayi da shi ta karshe sai da ya dauki lokaci mai tsawo yana nuna damuwarsa akan rashin tsaro da zaluncin da ake fama dashi a ƙasa.

Wani babban abin taƙaicin shine irin cin amana da kisan gillar da wanda ya kashe shi yayi. Soja ne mai suna Lcpl John Gabriel ya nemi cewa Mallam ya rage masa hanya daga Nguru zuwa Jaji-Maji. Kawai sai ya takatar da shi a cikin daji ya fito da bindiga ya masa har harbi uku. Sannan ya ja gawarsa ya jefar domin ya gudu da motarsa. Wada yace ba su yafe ba.

KUKUMA KARANTA: Yadda Sheikh Bagoni Aisam Gashuwa ya rasu

Amma da yake Allah Ya nufi bayyana walittakar bawansa Shaykh Bagoni, sai wannan barayon soja ya kasa tada motar. Har ma ya kira abokinsa mai suna Adamu Gideon su kayi ta fama amma mota taki tashi, kuma suka gagara guduwa har gari ya waye aka zo aka kama su. Ikon Allah kenan.

Jaridar Labarun Kafar Labaru ta rawaito cewar, daga bisani Barista Bulama ya kumayi addular Allah Ya karɓi shahadar Ustaz Bagoni, Ya sa Aljanna ce makomarsa Amen.

“Muna kira ga mahukunta da su gaggauta hukunta mara sa imanin da suka aikata wannan aika-aikar, “inji Bulama.

Sannan ya kumayi kira ga hukumar sojoji lalle su biya diyya ga iyalin mamacin domin da rigarsu da makaminsu wannan dan fashi yayi amfani kuma sakacinsu ne yasa wannan azzulumin sojan ya fito da bindiga ba don aiki ba, sai don yayi kisan gilla da fashi da makami.

Leave a Reply