Yadda Sheikh Bagoni Aisam Gashuwa ya rasu

1
294

Daga Saleh INUWA, Kano,

Mallam ya kamo hanya daga Kano zuwa Gashua. Yana zuwa bakin Barikin Soja na Nguru, sai yaga wani Soja me alamar yana jiran motar da zata ɗauke shi ne. Kazalika kuwa sai ya nemi alfarmar a rage musa hanya zuwa Jaji-Maji. Sojan yana ɗauke da irin gadon nan na tafida-gidanka (Camp Bed). Sojan yana cikin farinkaya ne ba inifam ba. Ashe akwai bindiga AK-47 cikin wannan Camp Bed shi Mallam bai ankara ba. Suna zuwa wani gari me suna Chakama sai Mallam yace zai sauka ya kama ruwa.

Sai wannan Soja me ɗauke da gado yayi amfani da wannan dama ya ciro bindigar yayi masa harbi har Uku nantake ya kashe shi. Bayan ya kashe shi, sai ya nemi wani abokin sa dake wajen da ya taimaka masa don su gudu da motar, amma sai motar taƙi tashi.

To su kuma mutanen wannan ƙauye da suka ji ƙara sun zata ma hatsari akayi, sai suka garzaya don su bada taimako sai suka fahimci asalin abinda ya faru. Nantake suka sanarda Jami’an tsaro suka kama waɗannan sojojin kuma yanzu haka suna nan Damaturu ana cigaba da bincike akansu.

Da bakinsa sojan da yayi kisan ya bayyana haka. Sunan sojan da yayi kisan Lance Corporal JOHN GABRIEL, shi kuma wanda yayi niyyar taimaka masa ADAMU GIDEON dake ƙarƙashin Bataliyar Soja ta 241dake Garin Nguru. Da aka tambayi sojan dalilin yin hakan sai yace yayi hakan ne don ya gudu da motar Mallam ɗin yaje ya sayar.

Gurin jana’izar

Tuni, anyi jana’izar sa a kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada, wanda jana’izar ta samu halartar mutane da dama.

1 COMMENT

Leave a Reply