Majalisa za ta gayyaci Ministar Kuɗi, gwamnan CBN da sauransu, kan matsalolin sufurin jiragen sama a Najeriya

2
435

Majalisar wakilan Najeriya za ta gayyato ministar kuɗi, Zainab Ahmed; da gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele; da Ministan sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Siriki da sauran masu ruwa da tsaki domin tattauna matsalar da ake fuskanta tsakanin gwamnati da kamfanin Emirates.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da majalisar ta fitar a jiya Juma’a.

A cewar sanarwar, za a yi wannan tattaunawa domin duba yada za a shawo kan matsalolin da ake samu tsakanin ɓangaren gwamnati da wasu kamfanonin jiragen ƙetare.

Wannan na zuwa ne bayan kamfanin jirgin Emirates ya sanar da dakatar da jigilar fasinjoji daga Najeriya.
Lamarin da ya sake daga hankulan fasinjoji, yayinda sufurin jiragen cikin gida ma ke fuskantar matsala saboda tsadar man jirgi na Jet A1.

2 COMMENTS

Leave a Reply