Idan har ASUU suka janye yajin aiki, sai karatun jami’a ya gagari talakawan Nijeriya – Farfesa Fagge

0
241

Farfesa Umar Sani Fagge Malamin addinin musulunci a jihar Kano ya bayyana cewa yajin aikin da malaman jami’o’i a Najeriya ke yi suna yi ne don maslahar al’umma ba wai maslahar kansu ba.

Shaikh Fagge wanda malami ne mai tawadhu’u, zuhudu da tsoron Allah, a yayin karatun da ya saba gudanarwa, ya ƙalubalanci Gwamnatin Najeriya cewa duk wata gwaninta da za ta yi ba za ta kai ta ilmi ba.

“Jama’a su wani wanda aka hana shi albashi sama da wata biyar ya hakura, in da maslahar malaman jami’a ce za su haƙura su janye. Ina tabbatar wa da duniya maslahar talakawa ce a ciki, wallahi idan suka janye da ƙyar kashi ashirin cikin ɗari na ‘ya’yan talakawa za su iya ci gaba da karatun jami’a. Sai dai Private, masu kuɗi ne kaɗai ‘ya’yansu za su yi karatu.

Duk abin da kuka sani a ƙasar nan gwamnati ta zare hannunta a ciki, kama daga lantarki, fetur da komai. Ilmin Primary da secondary ya karye na jami’an ne kawai a tsaye, shi kadai ne talaka ke ɗaukan wani abu, mu da muke koyarwa a jami’an ne muka san bala’in da jami’a suke ciki, da wahala ka sami department din da ba wasu malaman ne ke haduwa su biya wa wasu ɗaliban kudin makaranta ba, dubu talatin zuwa arba’in idan ka mayar da shi miliyan biyu waye zai iya biya?

Idan malaman jami’a suka janye, kowanne talaka sai ya biya sama da miliyan biyu. Don haka sai a yi addu’a don Allah ya haska wa gwamnatin ta gane lallai talaka ya kamata a cece shi a wannan lamari, duk inda gwamnati za ta zuba kuɗinta ba zai kai na wannan muhimmanci ba.

Ilmi kamar gishiri ne, idan ba kai ba miya. Ilmi mai gyaran zamani, idan babu shi ba inda ƙasar za ta je, kuma kullum gwamnati ita ce ɗakko wasu ƙwararru daga wasu ƙasashe ana ɓarnatar da kudi.” In ji Farfesa Sani Umar Fagge.

Leave a Reply