Daga Fatima GIMBA, Abuja
Al’ummar jihar Kano a arewacin Najeriya na ci gaba da bayyano ra’ayoyinsu dangane da yadda aka yi ta mamakon ruwan sama na kwanaki uku a jere.
Ruwan saman ya tsayar da harkokin ciniki da dama a babban birnin jihar. Ba kasafai ba dai ake samun mamakon ruwan sama da za a jera irin wadnan kwanaki har uku ana ruwa ba, da ya wuce awanni ba.
Wannan mamakon ruwan saman da aka samu a jihar ya jefa wasu daga cikin iyali halin ƙunci sakamakon rashin samun damar fita a samo abin kai wa baka saboda ruwan da ake yi.