Uwar da aka kamata da saurayin ‘yarta suna lalata ta yi bayani

0
525

Idan masu karatu basu manta ba, mun kawo muku labarin wata uwar da tayi abun kunya inda ‘yar Cikinta ta kama saurayinta da Mahaifiyarta, to ita uwar ta yi bayanin yadda abun ya faru.

Ta ce, “tabbas na biyewa raina, amma a gaskiya ina ƙaunar saurayin ‘yata tun ranar da ta soma kawo mini shi a matsayin wanda zai aureta, tun daga wannan ranar raina ya kasa hakura a kansa”, Inji uwar Yar.

KU KUMA KARANTA:Budurwa ta yi ma saurayinta duka bayan ta kama shi da mahaifiyarta a Abuja

Ta ci gaba da cewa, ” Na yanke shawaran na yaudareshi ne domin na haramta masa auren ‘yata. Hakan yasa na bar ƙofar ɗakin a buɗe yadda zata ganmu.

Sai dai ba kamar yadda ita ta faɗawa duniya ba wai ta kama mu turmi da taɓarya. Ban yi zina da shi. Ta dai ganshi a tuɓe babu komai a jikinsa sai ƙaramin wandonsa. Ni kuma na ɗaura zani a ƙirji, wannan yasa ta yanke hukuncin zina mu ke yi”.

Sai da uwar ta ce ta rarrashi yar tata daga baya kuma ta faɗa ma ta gaskiyar abunda ke ranta na ta bar ma ta saurayin nata, ita ta aureshi.

Sai dai mai tsaigunta mana labarin bai samu bayanin ko ɗiyar ta yarda ta barwa uwar tata ba, ko kuma har yanzu tana son saurayin na ta.

Leave a Reply