Najeriya za ta zama ƙasa me samar da iskar gas ga ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) yayin da ake ci gaba da gwabza yaƙin Rasha da Ukraine, wanda da aka fara a ƙarshen watan Fabrairu.
Tawagar EU a Najeriya da ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirka, ECOWAS, ne suka bayyana hakan a ƙarshen mako.
Mataimakin Darakta-Janar, Sashen Kula da Makamashi, Hukumar Tarayyar Turai, Matthew Baldwin ya yi wa manema labarai ƙarin haske a Abuja.
Baldwin ya je Najeriya ne domin ganawa da jami’an gwamnati da ‘yan wasa masu zaman kansu, ciki har da masu ruwa da tsaki a fannin makamashi.