‘Yar Afirka ta karya tarihin shekaru 571 a Birtaniya, inda tayi digirin digirgir a fannin likitanci

0
278

Kristyn Carter ta zama baƙar fata ta farko da ta kammala digiri na uku a fannin rigakafi a Jami’ar Glasgow, Burtaniya. A cewar Dr. Kristyn, Dokta James McCune Smith ne ya zaburar da ita, wanda ya zama Ba’amurke na farko da ya samu digirin digirgir a jami’a a shekarar 1837.

Da take magana da jami’ar Glasgow, Dr. Kristyn tace tana fatan zaburar da wasu ta wannan hanya, musamman matasan Afirka. A cikin kalamanta: “A cikin 1837, Dr James McCune Smith ya kammala karatu daga Jami’ar Glasgow, ya kafa tarihi a matsayin Ba’amurke na farko da ya sami digiri na likitancin Jami’ar. “A yau, na kafa tarihi a matsayin baƙar fata na farko data kammala digiri na uku a Jami’ar Glasgow a fannin Immunology.

Kasancewa baƙar fata taa farko, na kowane jinsi, data kammala karatun digirin digirgir babbar daraja ce, kuma ina alaƙanta ta duka ga Dr McCune Smith. “Nice taa farko, kuma ba zan zama ta ƙarshe ba, kuma ina fata kawai labarina ya isa ya zaburar da mutane da yawa su halarta”.

Leave a Reply