‘Yan daba sun kaima ‘yan majalisar Bauchi hari

Daga Fatima Gimba, Abuja

Wasu ’yan daba wanda sun kai kimanin guda 50, a ranar Litinin din da ta gabata, sun kai hari kan ‘yan majalisar dokokin jihar Bauchi, a yayin da suka taru a wani masaukin baki da ke kan titin Sir Kashim Ibrahim da ke da tazarar ‘yan mitoci daga gidan gwamnatin jihar Bauchi.

An ruwaito cewa mutane 6 sun jikkata, kuma ‘yan daban sun haddasa bala’in barna a wurin ta hanyar fasa gilasai da motoci da misalin karfe 4:00 na yamma.

Bayan afkuwar lamarin, nan take aka aike da tawagar jami’an tsaro daga rundunar ‘yan sandan Najeriya, da jami’an tsaron farin kaya, da na Civil Defence, da DSS, da kuma sojojin Najeriya, zuwa majalisar inda suka mamaye harabar ginin.

Bayan faruwar hakan, matakan tsaro ya tsaurara a yankin, inda aka girke tawagar da ta haɗa da jami’an ‘yan sanda, jami’an tsaro na farin kaya (DSS), da kuma sojojin Najeriya.

Hakan ya faru ne bayan da wasu da ba a san ko su waye ba, suka yi yunƙurin ƙona harabar majalisar, amma jami’an tsaro sukai gaggawar hana su.

Rahotanni sun nuna cewa ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Burra a karamar hukumar Ningi a jihar, Ado Wakili, yana ɗaya daga cikin wadanda suka jikkata. Ya yi zargin cewa ‘yan bindigar na dauke da bindigogi da wasu muggan makamai.

An ambato shi yana cewa, “Muna cikin wani ɗakin taro, kwatsam sai muka ji hayaniya da buge-buge a kofar gidan, yayin da muka fito don ganin abin da ke faruwa, ‘yan bindigar suka ruga riƙe da bindigogi, kwalabe da sauran muggan makamai.

“Dukkanmu mun yi kiɗime da gudu domin tsira da rayukanmu, kuma a cikin haka, da yawa daga cikinmu, har da ni, mun ji rauni, kamar yadda kuke gani a fuskata da ke karkashin idona.” Sunyi ɓarna ta gaske, sun rikita komai. A lokacin da muka fito, sun farfasa dukkan motocinmu da tagogin gidan.”


Comments

One response to “‘Yan daba sun kaima ‘yan majalisar Bauchi hari”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *