Yadda Sarkin Farisa ya yanke hukuncin feɗe fatar alƙali da ransa

0
715

Wannan wani zane na karni na 16, dake nuna fatar jikin wani alƙali da yayi rashin daraja, me suna Sisamnes, a shekara ta 500BC.

Sisamnes ya kasance alƙali mai cin hanci da rashawa a lokacin Cambyses ll a Farisa. An gano cewa ya karbi cin hanci a kotu kuma ya yanke hukuncin da bai dace ba.

Saboda haka ne sarki ya ba da umarnin a kama shi da laifin cin hanci da rashawar, sannan ya ba da umarnin a yanke fatarsa da ransa kafin a kashesa, domin yaji raɗaɗin cirewar.

Kafin yanke hukuncin, sarki ya tambayi Sisamnes wanda yake so ya nada a matsayin magajinsa. Sisamnes, a cikin son kansa, ya zaɓi ɗansa, Otanes. Sarki ya yarda, kuma ya nada Otanes ya maye gurbin mahaifinsa.

Bayan an zartar da hukuncin, Sarkin ya kuma ba da umarnin a yi amfani da fatar Sisamnes da aka cire, don lulluɓe kujerar da sabon alkali zai zauna a kotu. Yayi hakan ne domin tunatar da shi illar cin hanci da rashawa.

Wannan yasa dole Otanes, ya dinga tunawa a koyaushe, yana zaune a kan fatar mahaifinsa da aka kashe. Wannan ya taimaka wajen tabbatar da adalci da daidaito a cikin dukkan sauraren ƙararsa, shawarwarinsa da hukunce-hukuncensa.

Leave a Reply