Daga; Isah Ahmed, Jos.
SHUGABAN jam’iyyar PDP na Karamar hukumar Toro da ke Jihar Bauchi kuma Shugaban Kungiyar shugabannin kananan hukumomin Jihar Bauchi na jam’iyyar PDP, Alhaji Usama Aliyu Wundi, ya bayyana cewa alhakin ‘yan Najeriya ne ya kama Jam’iyyar APC, don haka ta shiga halin da take ciki na rudani da rikice-rikice. Alhaji Usama Aliyu Wundi, ya bayyana haka ne a lokacin da take zantawa da wakilinmu.
Ya ce Jam’iyyar APC ta yaudari al’ummar Najeriya, domin duk alkawurin da suka yiwa ‘yan Najeriya basu cika ko daya ba. Mulkin APC kamar zaman kurkuku ne ga ‘yan Najeriya.
“Wannan abu da su ka yi, ba zai tafi a banza ba domin Allah ba zai bar su haka ba, don haka suka fada jarrabawa, yanzu babu Jihar da basa cikin rikici a Najeriya. Ka dubi rudanin da suka shiga a zaben fidda gwanin na shugaban Kasa. Dubi yadda suka kasa zaben wanda zai tsaya masu takarar mataimakin shugaban Kasa”.
Alhaji Usama ya yi bayanin cewa karshen yaudarar da APC ta yiwa ‘yan Najeriya yazo domin yanzu sun dawo daga rakiyar ta.
Ya ce tsayar da Atiku Abubakar a matsayin Dan takarar shugaban Kasa da Jam’iyyar PDP ta yi alheri ne ga Najeriya, domin ya san dukkan wani lungu da sako na Najeriya, kuma ya san duk wani mataki na gwamnati a Najeriya.
Ya ce babu shakka ya san ‘yan Najeriya zasu zabi Atiku Abubakar a matsayin shugaban Kasa da kyakyawar niyya, a zabe mai zuwa na shekara ta 2023.