Gamayyar Al’ummar Arewa Sun Buƙaci Tinubu Ya Dauki Dogara A Matsayin Abokin Takarar Shi

0
573

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

WATA gamayyar Kungiyoyin al’ummar Arewa da ke fafutukar tabbatar da zaman lafiya da ci gaba (CFPP), sun buƙaci dan takarar Kujerar Shugaban Kasa, a karkashin Jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da ya dauki tsohon kakakin Majalisar Wakilai na Tarayya, Honarabul Yakubu Dogara a matsayin abokin takarar shi na zabe mai zuwa a shekarar 2023.

Gamayyar Kungiyoyin wanda a ranar Asabar suka gudanar da wani taron manema labarai a sakatariyar Kungiyar Yan Jaridu ta Najeriya (NUJ), reshen Jihar Kaduna, sun bayyana goyon bayan su ga tsohon dan Majalisar wanda su ka kuma bayyana shi a matsayin wanda ya fi kowa cancantar zama a matsayin mataimakin Shugaban Kasa ga dan takarar Jam’iyyar ta APC.

Da yake jawabi a wajen taron a madadin sauran al’ummar, Shugaban gamayyar Kungiyoyin ta (CFPP), Dakta Muhammad Chindo, ya jaddada bukatar su na cewa dole ne mataimakin dan takarar Kujerar shugabancin Kasar a karkashin jam’iyyar ta APC ya zama Kirista ne, kuma shi Honarabul Dogara ne wannan mutumin.

Gamayyar Kungiyoyin, wadanda tare da magoya bayansu akalla sama da mutane 70 wadanda suka hada da maza da mata da suka halarci wannan taron, sun zabi goyon bayan tsohon kakakin majalisar wakilai ta tarayya Rt. Hon. Yakubu Dogara ne a matsayin Kiristan da ya fi kowanne dacewa.

Kodinetan kungiyar na kasa, Dokta Muhaamad Chindo, ya kara da cewa mataimakin shugaban kasa na gaba, ya nunar da cewa dole ne mataimakin ya zama kirista wanda ya zarce ra’ayin kowa a tun farko wanda rashin yin hakan na da nasabar kawo rudani a cikin addini da sharri na kabilanci da bangaranci.

Gamayyar ta kuma bayyana cewa, a bisa la’akari da nau’o’in daban-daban na Najeriya, da kuma bukatar tabbatar da adalci da kasancewarsa mafi dacewa, dole ne wanda za a zaba a matsayin mataimakin shugaban kasa ya kasance wanda yake da halayen da ake bukata da kuma kwarewa a siyasance.

A cewar gamayyar, irin wannan mutumin dole ne ya zama Kirista nagari wanda ya hada kai wajen samar da hadin kaia tsakanin al’ummar kasarmu daban-daban.

Sun kara da cewa, bayan kammala bincike da kwazo, domin ci gaba da jajircewarsu da sadaukarwar da suka yi wajen ganin an tabbatar da dunkulewar Najeriya, gamayyar ta kammala da cewa Rt. Honarabul Dogara shi ne mutumin da yafi cancanta da mukamin mataimakin Shugaban Kasa a karkashin Jam’iyyar ta APC.

A cewarsu zabin Dogara a matsayin wanda ya fi dacewa ya samo asali ne daga wasu dalilai guda biyar da suka zabe shi kuma suka yi magana da shi na tsawon shekaru har sai da radin kansa ya sauka, a matsayinsa na dan siyasa wanda aka gwada kuma aka amince da shi, wanda ya gina gada da amincewar mazabar DASS. /Tafawa Balewa/Bogoro na mutane daban-daban, kana ya gina masallatai ga musulmi fiye da coci da sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here