JABIRU A HASSAN, Daga Kano.
SHUGABAN Gidauniyar Tamallan, Dokta Saleh Musa Wailare ya nuna jindadin sa bisa yadda bukukuwan ranar Yara ta duniya suka gudana a kananan hukumomin Dambatta da Makoda a ranar Juma’ar da ta gabata.
A cikin sakon da ya aika ga yaran wannan yanki, Dokta Saleh Musa Wailare ya bayyana cewa yara sune abin alfaharin al’umma duba da yadda Allah ya albarkace su da basirar mallakar ilimi da tarbiyya a matsayin su na manyan gobe.
Ya ce ” Ina mai bayyana jindadi na bisa yadda bukukuwan tunawa da ranar Yara suka gudana a kananan hukumomin Dambatta da Makoda, sannan na yaba kwarai da gaske bisa yadda aka shirya bikin duba da muhimmancin yaran mu wadanda wata rana sune shugabannin al’umma” inji shi.
Haka kuma Dokta Wailare ya hori iyaye da masu rike da yara da su kara sanya idanu Kan yaran su ta yadda zasu ci gaba da kasancewa masu tarbiyya da Kuma kaucewa shiga hulda da bata gari, inda ya jaddada cewa Gidauniyar Tamallan zata ci gaba da shirya wannan bukukuwa duk shekara domin samar da farin ciki a zukatan yaran mu masu tasowa.
Wakilin mu wanda ya ziyarci wasu guraren ya ruwaito cewa bukukuwan sun yi kyau da tsari duba da yadda wadanda suka shirya bikin a kananan hukumomin Dambatta da Makoda suka tsara yadda aka gudanar da bukukuwan cikin nasara.
Sannan dukkanin yaran da suka zanta da wakilin namu sun sanar da cewa bikin na bana yafi na bara armashi saboda yara sun rabauta daga kayayyaki iri-iri domin su kara himma wajen neman ilimi da tarbiyya.
A karshe, wasu daga cikin iyaye da suka tattauna da wakilin mu, sun nunar da cewa ba zasu manta da wannan rana ba saboda yadda suka hadu da abokan karatun su domin jaddada zumunci da kaunar juna ta sanadiyyar Dokta Wailare, tare da fatan Allah ya kai mu na shekara mai zuwa idan Ubangiji ya Kai mu.