Gamayyar Kungiyoyin Ma’aikatan Masakun Kaduna Sun Koka Kan Rashin Biyan Hakkokinsu

0
326

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

GAMAYYAR kungiyar ma’aikatan Masaku da aka kulle ba tare da biyansu hakkinsu ba a jihar Kaduna, sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Kaduna da su gaggauta kawo musu dauki ta hanyar biyansu hakkokinsu da ba a biya su ba domin samun ingantacciyar rayuwa ga ‘ya’yansu.

Da suke jawabi yayin wani taron zanga-zangar lumana da aka shirya a harabar Kaduna Textiles Limited (KTL) a ranar Alhamis, ma’aikatan sun nuna damuwarsu kan shiru da suka dade su nani wanda yake kashe su a kullum tun bayan rufe masana’antar sama da shekaru 20 da suka gabata.

A cewar shugaban gamayyar, Kwamared Jeibe Wordam Simdik, ya bayyana cewa aikin masaku a Kaduna da wasu sassan Najeriya sun bayar da gudunmawa sosai wajen habaka tattalin arzikin kasa.

Ya kara da cewa, tun bayan rufe wadannan masana’antun da aka rufe, sun fuskanci munanan kalubale da suka hada da rashin lafiya, tabarbarewar ilimin ’ya’yansu, lalacewar aure, matansu da ‘ya’yansu sun zama mabarata ta hanyar barace-barace domin ciyar da su.

“Ma’aikatanmu sun zama abokan cinikin kotun saboda rashin biyan kudin haya.
Bisa la’akari da abubuwan da ke faruwa, da yawa daga cikin ma’aikatanmu da danginmu suna mutuwa cikin takaici saboda haka, muna kira ga duk masu ruwa da tsaki a Najeriya da su jikanmu tare da yin adalci a cikin halin da muke ciki.”

“Sake bude duk wasu masakun da aka rufe a Najeriya da suka hada da Kaduna Textiles Limited, Arewa Textiles PLC, NORTEX Nigeria Limited, da FINETEX Limited, zai samar da damar aiki ga hadakar matasa da kuma rigakafin rashin tsaro a Najeriya.” Ya Jaddada

“Shugabanninmu na yanzu da suka jagorance mu sama da shekaru 20, wani abun dogaro suka bar wa ‘ya’yanmu, saboda kin biyan mu hakkinmu bayan sun yi shekaru da dama suna hidima.” Inji Comrade Jeibe

A cewarsa, shugaban kasa Muhammad Buhari ya yi mana alkawarin cewa duk masana’antun za a farfado da su amma an yi watsi da mu. Hakazalika Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa’i ya yi alkawarin farfado da rufaffun masaku a lokacin yakin neman zabensa a shekarar 2015 da 2019, amma duk an watsar.

“Muna kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, shugaban kungiyar gwamnonin Arewa kuma shugabanin majalisar wakilai ta kasa da su tausaya tare da yin adalci su biyamu hakkinmu.”

“Muna kira ga masu wannan masana’antar da aka rufe da su biya mana bukatunmu domin muna son iyalanmu su kasance cikin rayuwa mai kyau kamar sauran al’ummar Najeriya.” Ya koka

A karshe, mambobin kungiyar da ke karkashin inuwar gamayyar kungiyar sun yi alkawarin cewa daukacin ma’aikatan da ke aikin masaku sun sha alwashin yin amfani da katin zabensu wato P.V.C wajen zaben 2023 ga wadanda za su yi la’akari da halin da suke ciki yanzu don kawo musu dauki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here