Najeriya Na Da Bukatar Tsayayyen, Jajirtaccen Mutum Kamar Ni – Bukola Saraki

0
437

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

A BISA yunkurin da yake na ganin cewa ya samu shugabancin Kasar Najeriya, Tsohon Gwamnan Jihar Kwara kuma Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Dakta Abubakar Bukola Saraki, ya yi ikrarin cewa Kasar Najeriya na da bukatar tsayayyen mutumi kuma jajirtacce wanda zai iya kai ta ga tudun mun-tsira.

Dan takarar Shugabancin Kasar Najeriya, Sanata Bukola Saraki, ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da wakilan Jam’iyyar PDP a garin Kaduna, a ranar lahadi domin neman goyon bayansu a bisa kudirinsa na neman Jam’iyyar ta tsayar da shi a matsayin dan takarar ta.

Ya kara da cewa kamar yadda kowa ya sani, shi mutum ne wanda yake mai kishin al’umma kuma jajirtacce wanda ya saba nuna bajintarsa a fagen daga wajen ganin ya kare hakkin al’umma tare da kawo musu ci gaba ta kowani fanni don tabbatar da adalci a tsakaninsu.

Ya ce “shekarar 2023, lokaci ne da ba za ace an zabi kowani irin mutum ba a matsayin Shugaban kasa, kuma duk mun san cewa babu ta yadda za ayi a samu mulki ba tare da sa albarkarku yan Kaduna ba saboda mahimmanci ku, don haka nayi takakkiya na kawo kaina domin neman amincewa da goyon bayan ku ta yadda zan zama Shugaban Kasar Inshaa Allahu.”

“Wannan Kasar na cikin mummunar yanayi kuma babu wanda ya fi ku yan Kaduna sanin wannan yanayin domin a shekarun baya, ba dare ba rana mutane na iya zirga-zirga amma yanzu lamarin rashin tsaro ya lalata al’amura, saboda haka nake son ku bani damar da zan yi gyaran da zai canza al’amura ta yadda za a samu waraka wajen tafiyar da al’amura.”

“Wannan kasar nan na da bukatar wani jajirtaccen mutum wanda Kasar ce kawai a zuciyarsa kuma a shirye yake da ba da rayuwarsa wajen ganin ya yi halacci ga al’umma tare bunkasa dukkan al’amura da tattalin arzikin Kasar, kuma kunsan na kasance mutum ne wanda ya ke dauke da duka irin wadannan shiffar musamman a lokacin da nake Shugaban Majalisar Dattawa.

“Kuma a matsayina na likita, na yi muku alkawarin cewa muddun kuka zabe ni har na kai ga zama Shugaban kasa, zan tabbatar da duk wani dan kasa na zuwa asibiti kyauta, musamman iyayenmu mata domin wannan wani abu ne da na taba jaraba shi kuma yayu ayayin da nake Gwamna a Jihar Kwara, sannan na yi alkawarin kawar da duk wata matsalar tsaron da kuke fuskanta ana Kaduna.

“Ba zan taba gajiyewa ba har sai naga na tabbatar da na kawar da matsalar rashin tsaro da ta’addanci ta yadda kowa zai iya gudanar da harkokinsa ba tare wani shakku ko tsoro ba, yaranku su je Makaranta cikin kwanciyar hankali domin a yanzu talauci ya yiwa al’umma yawa, babu kwanciyar hankali don haka muke bukatar wannan canjin wanda ni zan kawo muku shi cikin yardar Allah.

Sanata Abubakar Bukola Saraki, ya godewa Ya’yan Jam’iyyar PDP ta Kaduna, bisa irin karamcin da suka nuna mishi tare da neman tabbacin goyon bayansu na ganin ya cimma nasarar wannan kudirin nasa na zama Shugaban Kasar Najeriya a zaben shekarar 2023 mai zuwa.

Da yake jawabi amadadin Dattawan Jam’iyyar PDP na Jihar Kaduna a wajen taron, tsohon Gwamnan Jihar, Dakta Muktar Ramalan Yero, ya yabawa dan takarar bisa ziyarar tare bayyana cewa, tabbas shi mutum ne mai natija da rike alkawari, kana jajirtacce wanda ya nuna kwazonsa a baya kuma zai iya yin duk wani abu na ganin cewa ya ciyar da kasar gaba.

Dallatun Zazzau, ya ci gaba da cewa, a irin sanin da ya yiwa Dan Takarar Kujerar Shugabancin kasar, a matsayin abokin aiki, Shugaban Gwamnoni da abokinsa, mutum ne wanda yake da kwarewa ta fanni daban-daban kuma yake Kokarin ganin ya aiwatar da al’amura yadda ya kamata, don haka suna fatan idan Allah Ya kai shi ga zama Shugaban Kasar, ya tabbatar da an kawar da matsalar rashin tsaro daya addabesu a Birnin Gwari don wannan ita ce babbar matsalar su.

A karshe, Ramalan Yero, ya tunatar da Dan takarar Sanata Abubakar Bukola Saraki da cewa ya sani Mulkin na Allah ne, amma suna goyon bayan shi dari bisa dari domin tabbatar da ya kai ga samun shugabancin Kasar a zaben shekarar 2023 mai zuwa cikin yarda da ikon Allah.

Leave a Reply