Tsaftace Dimokuradiyya Zai Samar Da Shugabanci Nagari – Inji Gambo Sallau

0
723

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

TSOHON Shugaban majalisar dokokin jihar Kano Alhaji Gambo Sallau ya bayyana cewa idan aka tsaftace dimokuradiyyar kasarnan, za a sami shugabanci nagari musamman ganin cewa Najeriya kasa ce da take tafiya Kan tsarin dimokuradiyya.

Yayi wannan tsokacin a cikin hirar su day wakilin mu, inda ya nunar da cewa idan aka bi sahihin tsarin da dimokuradiyya take da shi, ko shakka babu za a ci gaba da tafiya kan kyakykyawan jadawalin kawo ingantaccen sauyi a siyasan ce da Kuma zamantakewar al’umma.

Alhaji Gambo Sallau ya Kara da cewa ” akwai bukatar ganin an ci gaba da baiwa tsarin dimokuradiyya kulawa ta musamman domin aiwatar da harkokin siyasa domin samar da ci gaba, don haka tsarin dimokuradiyya yana bukatar tsafta da kuma tsarin daidaita manufofin ci gaban kasa”. Inji shi.

Tsohon Shugaban majalisar ya kuma bayyana ajiye aiki da masu rike da mukaman siyasa a Jihar kano suka yi, Gambo Sallau yace yadda aka sauka da yawa alamu ne cewa dimokuradiyya tana Kara cimma nasara fiye da yadda abin yake a baya, tareda jaddada cewa akwai kyakykyawan zaton cewa a shekara ta 2023 za a sami shugabanni na kirki a wannan kasa.

Dangane da batun matasa a siyasar Najeriya kuwa, Alhaji Gambo Sallau ya sanar da cewa lokaci ya yi da matasan zasu kara fito da kansu da akidojin su na kawo ci gaban kasa da kuma al’umma duk da cewa yana dakyau su kara samun kwarewa da sanin makamar aiki daga malaman su na siyasa kamar yadda ake gani a wasu sassa na duniya da matasan ke jagoranta.

A karshe, Alhaji Gambo Sallau ya yi kyakykyawan zaton cewa zaben shekara ta 2023 zai kasance alheri ga al’umma musamman ganin cewa kowane dan kasa yana bukatar a kara samun zamantakewa mai albarka.

Leave a Reply