Gwamnatin Buhari Ta Gyara Harkokin Mai, Wutar Lantarki Da Jami’o’i Kafin Ta Sauka – Dokta Isma’ila

0
330

Daga; Isah Ahmed, Jos.

WANI Malami a sashin nazarin tattalin arziki na Jami’ar Jihar Bauchi, Dokta Isma’ila Bello Usman, ya bukaci Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta yi kokari kafin ta sauka, ta magance matsalar harkokin mai da wutar lantarki da Jami’o’in kasar nan. Dokta Isma’ila Bello Usman, ya bayyana wannan bukata ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

Ya ce kamar a bangaren mai gwamnatin ta yi kokari, ta gyara koda matatun mai biyu a kasar nan, wadanda zasu rika samar da man da za a rika amfani da shi, ba tare da zuwa waje ana shigo da shi ba.

Ya ce a bangaren wutar lantarki, Gwamnati ta dubi kamfanonin da ta damka alhakin raba wutar lantarki a kasar nan, don warware matsalolin da ke kawo rashin wuta a Najeriya.

Dokta Isma’ila ya yi bayanin cewa a bangaren jami’o’in kasar nan, gwamnati ta zauna da malaman jami’o’i, domin warware matsalolin da suke sanya suke tafiya yajin aiki.

“Babu shakka idan gwamnatin nan ta gyara wadannan abubuwa guda uku, al’ummar Najeriya zasu rika tunawa da ita kan tayi masu wani abu na cigaba. Amma idan har gwamnatin nan ta tafi, ta bar wadannan abubuwa ba tare da warware su ba, al’ummar Najeriya zasu rika tunawa da ita a matsayin wadda ba ta yi masu komai ba”.

Malamin Jami’ar ya yi bayanin cewa, gaskiya tattalin arzikin Najeriya ya sami matsaloli da dama a zamanin wannan gwamnati musamman ta hanyar tsare tsaren ta na yaki da cin hanci da rashawa da rufe kan iyakokin kasar nan da kara farashin mai. Don haka farashin kayayyaki suka yi sama a Najeriya, kuma talauci yake karuwa a kasar nan.

“Allah ya albarkaci Najeriya da dukiya sai dai tsarin tattalin arzikin kasar ne kawai, wanda yake masu kudi suna kara kudancewa, talakawa kuma suna kara talaucewa”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here