Shugabancin Najeriya 2023: PDP Za Ta Bude Kofar Takara Ga Kowa

0
387

ALAMU sun nuna cewa babbar jam`iyyar hamayyar Najeriya wato PDP za ta bar kofa bude ga dukkan `ya`yanta da ke sha`awar takarar shugaban kasa daga kowane bangaren kasar su fafata.

Sai dai kokawar da masu neman takarar ke yi na neman raba kan `ya`yan jam`iyyar.

A halin da ake ciki lamarin ya raba jam`iyyar gida uku kuma siyasa na cewa kokawar za ta iya shafar makomar PDP a babban zabe mai zuwa.

Duk da cewa ba a san adadin masu neman takarar shugaban kasa a tutar jam`iyyar PDP ba, kasancewar jam`iyyar ba ta dakatar da sayar da fom ga masu bukata ba, sai dai take-taken fitattu a tsakanin wadanda suka riga suka bayyana aniyarsu ta neman takarar da su da magoya bayansu na neman raba jam`iyyar gida uku.

Rukunin farko ya kunshi gwamnan jihar Rivers da wasu gwamnoni da ke da ra`ayin lallai ludayi ya kewaya, wato sai mulki ya koma kudancin Najeriya.

Sai bangaren wasu masu neman takarar daga arewacin Najeriya, da ya hada da gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, da na Bauchi, Sanata Bala Muhammad, da kuma tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki, wato rukunin masu ra`ayin maslaha, wadanda ke bukatar su daidaita a bar takarar ga mutum guda.

Sai kuma bangare na uku, wanda wasu ke masa kirari da kai-kadai-gayya wato rukunin tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar da nasa magoya bayan.

Haka wadannan gidaje uku suke da irin nasu magoya bayan, ciki har da gwamnoni masu ci da tsofaffi da sauran jiga-jigan jam`iyyar PDP.

Skip Podcast and continue readingPodcastKorona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Kowane bangare ya dukufa wajen neman takarar, har ma mafi yawansu na safa-da-marwar kai ziyara ga wasu tsoffin shugabnnin kasa da sauran masu karfin fada a ji a jam`iyyar.

Kuma ganin yadda idon kowane bangare ya rufe ne masana ke cewa abin da jam`iyyar PDP ke gudu ya faru. Dr Abubakar Kari, masanin siyasa ne a jami`ar Abuja, ya ce “Ita wannan rarrabuwar kai tana daukar kalar bangaranci ne, wannan abu ya ki ci ya ki cinye wa, yana da hadari kwarai da gaske ga jam’iyyar kuma idan ba ta yi hankali ba wanki hula zai kai ta dare”.

Sai dai duk da cewa jam`iyyar PDP na ci gaba amfani da salon jan-rai wajen fadar yankin da za ta bai wa takarar shugaban kasa, masana na cewa ko ba jima ko ba dade, ba ta da zabi sai ta tsallake siradin…kuma idan ta yi sake sai a yi mata sakiya.

Wannan ne ya sa Dr Abubakar Kari ke cewa sai ta yi taka-tsantsan.

“Muddin jam’iyyar PDP ta na so ta kai labari, to dole ne ta yi taka-tsantsan. Bangaren da za ta bari ya yi takara da kuma wanda zai yi mata takarar zai iya zama ‘yar manuniya ga irin tabukawa ko rashin tabukawa da za ta yi a zabukan 2023.

“Alal misali idan suka zabi dan wani bangare, to wanda ba wannan dan bangare ba, za su iya juya mata baya ko kuma su ci gaba da zama a ciki amma suna ungulu da kan zabo”.

Masanin ya kuma kara da cewa idan jam’iyyar PDP ta dauki dan takara wanda ba mashuhuri ba, to kamar sun bude hanya ne ga jam’iyyar APC ta ci zabe a shekarar 2023.

Sai dai wasu jiga-jigan jam`iyyar PDP ta saba da shiga irin wannan matsatsin tana fita.

Sanata Ibrahim Umaru Tsauri, tsohon sakataren jam`iyyar ne na kasa, kuma ya shaida wa BBC cewa “Jam’iyyar PDP ba ta tsoron rikicin cikin-gida, idan an kawo matsayi a shiyyarku a kan zoning to duk wanda ya cancanci yin takara na tsayawa, idan dan takarar ya wuce daya to abin da mukan yi shi ne sai mu ce a zo a zauna a yi abin da ake kira ‘consensus’ wato a fid da mutum guda idan ba zai yiwu ba sai a je a hau layi a yi zabe”.

Kwamitin da PDP ta kafa don yanke shawara a kan maganar yankin da za ta bai wa takarar shugaban kasa dai ya ce ya gama aikinsa, amma bai fadi gangariyar matsayinsa ba sai lokacin da zai danka wa kwamitin zartarwar jam`iyyar rahotonsa, duk kuwa da cewa wasu sun tsegunta wa manema labarai cewa jam`iyyar za ta bar takarar a bude ga kowa da kowa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here